Dakunan saukan baki na kukan rashin mutane

Dakunan saukan baki na kukan rashin mutane

- Dakunan saukan baki a fadin kasa na kukan rashin jama’a sanadiyar matsin tattaliin arziki

- Zuwan mutane ota ya rage da kasha 35 cikin 100 da kuma mutane yanzu sun fi son shiga otal mara tsada

Dakunan saukan baki na kukan rashin mutane

[caption id="attachment_1060487" align="alignnone" width="300"] Transcorp Hilton Hotel, Abuja[/caption]

Wata rahoton da jaridar Thisday ta bayar yana nuna cewa manyan dakunan saukan baki a Abuja da Legas na kukan rashin zuwan mutane zama a otal sanadiyar matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Game da cewan rahoton , dukanan saukan baki irinsu Southern Sun, Intercontinental, Wheatbaker, Eko Hotel and Suites and Federal Palace,dukka a jihar Legas ne abin ya shafa.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa na ba Shugaba Buhari ciwon kai

A Abuja kuma, otal irinsu Transcorp sun kuka. A shekaran da ya gabata, otal din an alfaharin cewa dakunansu 80 cikin dari na cike amma yanzu abubuwa sun canza.

Matsalan shine otal din sun fara dakatar d ma’aikata saboda wannan matsala da suke fuskanta kuma domin cimma manufa.

“Matsalan yanzu, manyan otal na dakatad da ma’aikata su. Irinsu Southern Sun da Intercontinental , sai da suka kori ma’aikatansu sanadiyar wannan matsin tattalin arzikin. Yanzu mutane sun gwammace su shiga dakunan saukan baki wanda bai wuce N50,000 a dare daya ba.

“Yanzu suna zuwa otal irinsu Protea Chain a legas da Abuja. Saboda kudi maras yawa.

A biyomu a shafinmu na Tuwita :@naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel