Obasanjo yayi tsokaci game da gwamnatin Buhari

Obasanjo yayi tsokaci game da gwamnatin Buhari

- Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yaba da rawar da shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari ya taka wajen bai wa jami’an tsaro umurnin dirar mikiya kan manyan alkalan kasar da ake zargi da cin hanci da rashawa.

- Obasanjo ya ce kama alkalan ya nuna kwarin gwiwar da bangaran zartarwa ke da shi wajen tsaftace bangaren shari’a da tuni cin hanci ya dabaibaye shi.

Obasanjo yayi tsokaci game da gwamnatin Buhari
Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban wanda ya bayyana bangarorin da suka tabarbare da suka hada da Majalisa da kuma aikin gwamnati y ace duk da ya ke hanyar da aka bi wajen kama alkalan bai da ce, babu wata hanya ta dabam da za’a iya bi domin magance matsalar dole sai haka.

KU KARANTA: An sake kubuto wasu da yan Boko Haram suka sace

Cif Obasanjo ya kuma bai wa Buhari shawara da ya daina korafi kan abin da ya wuce, inda ya ce tun da an zabe shi ne domin ya gyara Nigeria, ya kamata ya mayar da hankali kan gyara barnar da ya tarar.

Obasanjo ya kara da cewa, cin zabe abu ne mai sauki idan aka kwatanta da gyara wata barna da aka tafka. Idan kana daga gefe abin da kake iya hangowa ba zai taba kamo kafar abin da ke nan a zahiri ba.

Haka kuma Obasanjo ya soki shirin da gwamnatin Buhari ke yi na ciwo bashin dala biliyon 30.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel