Jirgin shugaban kasa da aka ba sojin sama ya fadi a Makurdi

Jirgin shugaban kasa da aka ba sojin sama ya fadi a Makurdi

- Daya daga cikin jirgin shugaban kasa wanda aka ba hukumar sojin Najeriya a kwanan nan, Agusta AW 101, madaidaicin jirgi mai saukar ungulu wanda aka yi shi musamman domin aikin sojoji, ya yi hatsari a sansanin sojin saman Najeriya, Makurdi

- A cewar wani rahoto, jirgin ya yi hatsari ne sakamakon rashin horo mai kyau na ma’aikatan jirgin

- Jirgin ya samu gagarumin matsala amma ba’a rasa rai ba a hatsarin

Jirgin shugaban kasa da aka ba sojin sama ya fadi a Makurdi
Jirgin shugaban kasa da aka ba sojin sama da yayi hatsari

Daya daga cikin jirgin shugaban kasa wanda aka ba hukumar sojin Najeriya a kwanan nan, Agusta AW 101, madaidaicin jirgi mai saukar ungulu wanda aka yi shi musamman domin aikin sojoji, ya yi hatsari a sansanin sojin saman Najeriya, Makurdi

Hatsarin yazo ne watanni biyu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika jirgin yaki guda biyu daga cikin jiragen shugaban kasa ga hukumar sojin saman Najeriya.

Bisa ga wani rahoto daga TheNewGuru.com, jirgin ya fadi ne saboda rashin roho mai kyau ga ma’aikatan jirgin.

KU KARANTA KUMA: Kamfanonin Niger Delta zasu samu kwangilar NNPC

Bayan mika jirgin ga hukumar, an kuma fentin jirgin daga yanda take a da wato fari da kore zuwa ga kallan kayan sojoji.

Wata majiya ta bayyana wa shafin manema labarai cewa jirgin ya samu gagarumin matsala amma ba’a rasa rai ba a hatsarin.

Jirgin shugaban kasa da aka ba sojin sama ya fadi a Makurdi
Jirgin da yayi hatsari

Jirgin saman, Agusta AW101, wanda ya kasance babban jirgi mai saukar ungulu ya kai kimanin dala miliyan 21 (N1o.5billion)  ko wani daya wanda ya sa yafi madaidaicin jirgi tsada da kaso 130 cikin dari.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya umarci Danjuma ya kawo karshen rikici a Niger Delta

Amma Jami’I mai kula da alakar mutane na hukumar sojin saman Najeriya, Kyaftin Dele Famuyiwa, ya karyata rahoton cewa daya daga cikin jiragen ya fadi.

“Ba hatsari bane. Ba zan kirashi hatsari ba saboda kawai ya fadi ne a kasa a Makerdi.”

Yace fadin ba wai sakamakon rashin horon ma’aikatan jirgin da fasaha mai kyau bane cewa wadannan ma’aikatan ne dai suke kula da jirgin a fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel