Ko shin wanene sabon sirikin Buhari?

Ko shin wanene sabon sirikin Buhari?

- Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra za ta auri dan gidan hamshakin Attajirin nan, Muhammad Indimi

- Muhammadu Indimi kasurgumin Attajiri ne a Kasar Borno

- Ahmed Indimi yana daga cikin ‘ya ‘yan wannan mai kudi

Ko shin wanene sabon sirikin Buhari?

 

 

 

 

 

Ana ta samun rahoto cewa diyar Shugaban Kasa, Zahra Buhari za tayi aure nan da kwanaki kadan masu zuwa. Zahra Buhari dai tayi fice ko a cikin ‘ya ‘yan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Mun kawo maku bayani, ko shin wanene wannan sabon sirikin na Buhari?

Ahmed Indimi yayi karatun share fagen Digiri a Legas, a wata Makaranta ‘Global International’, daga nan ya wuce Jami’ar InterContinental ta Amurka da ke Atlanta domin yin digiri na farko a Bangaren Fasahar Komfuta da bayanai.

KU KARANTA: An gaishe da wannan Mahaifiyar

Ahmed Muhammad Indimi shine Shugaban Kamfanin ‘Oriental Energy Resources’ masu harkar Man fetur. Ahmed Indimi dai saurayi ne kyakkyawa kuma son kowa. Sannan Ahmed yana da ban dariya da kuma son dariya.

Ahmed Indimi mutum ne mai son karatun tsiya, bayan yayi digiri, ya koma yayi digiri na biyu kan harkar kasuwanci da ake kira MBA game da Harkar tsaron yanar gizo a Jami’ar nan dai ta Amurka. A wannan Makaranta ya rike matsayin Ma’aji na Kungiyar dalibai, Tun shekaru uku da suka wuce kuwa, Angon Zahra ya ba Miliyan dari baya. Kyaun da ya gaji uban sa, Ahmed Muhammad Indimi.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel