Sifeton yan sanda ya damu akan mutuwan hafsoshi 128

Sifeton yan sanda ya damu akan mutuwan hafsoshi 128

- Hukumar yan sandan Najeriya na shirin fito na fito da yan baranda bayan yan sanda 128 sun rasa rayukansu cikin watanni 3 kacal

- Sifeton yan sanda Ibrahim Idris yace wajibi ne akawao karshen wannan kuma a daina lalata dukiyoyin yan sanda

Sifeton yan sanda ya damu akan mutuwan hafsoshi 128

Sifeto-Janar na yan sanda, Ibrahim Idris yayi matukar nuna damuwarsa akan mutuwan hafsoshin yan sanda.

Yan sanda sun bayyana ta hanyar kakakinsu DCP Don N. Awunah a ranan laraba,Nuwamba 23 cewa sun rasa maáikata 128 a watanni 3 da suka gabata.

KU KARANTA: Kaji abin da wata uwa tayi domin ta tura yaro makaranta

Jawabin wacce jaridar Legit.ng ta samu ya bayyana cewa Sifeto janar na yan sanda Ibrahim Idris yay i matukar damuwa akan alámarin .

Jawabin tace:

“Sifeto Janar nay an sanda, Ibrahim Idris NPM, mni, ya siffanta kisan jamián yan sanda a bakin aikinsu a matsayin babban abun damuwa. Wannan kisan gillan da yan daba ,yan baranda ke yiwa mutanen mu wajibi ne a kawo karshen shi.

“Wani abun bacin ran shine yadda ake lalata kayan yan sanda da dukiyoyinsu. Wata sabuwar harin da aka kai a kauyen Dankamoji na karamar hukumar Maradu a jihar Zamfara, Abagana a jihar Anambra, Okrika a jihar RInas. Inda aka kasha yan sanda kuma aka lalata dukiyoyoinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel