Hindatu Umar tace tana son inganta ilimin mata

Hindatu Umar tace tana son inganta ilimin mata

An haifi Hindatu a Argungu, ta yi karatu a makarantar Islamiyya ta Malam Ladan da ke cikin unguwarsu a nan Argungun, daga bisani ta zarce zuwa makarantar Firamare ta ‘GTC Primary School’ duk a cikin garin Argungu.  Bayan ta kammala karatun firamare, ba ta bata lokaci ba, ta wuce zuwa makarantar Sakandire ke nan. Ta fara a Argungu, ta kammala a Sakandaren da ke garin Aleiro.

Bayan kammala karatunta ne ta fara aiki a karamar Hukumar mulki ta Argungun. Tana nan ne sai ta tsunduma a siyasa. Tana cikin harkokin siyasar ne har Allah ya kai ta ga matsayin Kansila ta riko, daga nan aka yi mata mataimakiyar Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Argungu. Ba a jima ba, Gwamna Jihar, Atiku Bagudu ya sauke kantomomi, sannan ya umarci duk kantoma ya bai wa mataimakinshi zuwa i yanzu.

Yayin da wasu ke farin ciki da sambarka da nadin nata, wasu kuwa korafi suka rika yi, sakamakon abin da suka kira karancin shekarunta da rashin gogewa a fagen siyasa da mulki.

Hindatu Umar tace tana son inganta ilimin mata
Hindatu Umar

To, duk da gutsiri tsoma da aka ta yi, Hajiya Hindatu dai ta ci gaba da kasancewa Kantomar aramar Hukumar Argungu, a matsayin mafi karancin shekaru da ke rike da mukami irin wannan a duk fadin Nijeriya.

KU KARANTA KUMA: Ina tare da Buhari da APC- Tinubu yayi gargadi

Da akayi mata tambayoyi game da wasu abubuwa ga abunda ta fada:

Zan fara sunan Allah mai Rahama mai jinkai. Ba zabena aka yi bisa mukamin Kansila ba, nadi aka yi min a matsayin rikon kwarya.

Alhamdulillahi. Allah abin godiya. Mulki Allah ne ke ba da shi da kuma goyon bayan jama’a. Allah ya ba ni wannan mulki ba iyawata ba, ko wayo na, ko dabarata ba. Ni ban taba tunanin zan kawo haka ba.

Kalubalen da na fuskanta shi ne wajan masu fadin karancin shekaru na.

Ni shekara ta 27 da haihuwa, domin an haife ni a 1989 zuwa yanzu kun ga kimanin shekara ashirin da bakwai ne.

Zan yi kokari na ga na taimaka musamman wajen samar da ilmin ‘ya mace, sai ta fannin lafiyarsu zan yi iya kokarina na ga na samar masu da lafiya mai dorewa kawai hadin kansu na ke ni ma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel