An sauke sunan Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar PDP

An sauke sunan Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar PDP

- Kotun daukaka kara dake garin Abuja ta sauke sunan dan takaran neman gwamna na jahar Ondo a karkashin jam'iyar PDP wato Jimoh Ibrahim a zaben da za'ayi a ranar Asabar

- Haka kuma kotun ta amince da bayanin wannan lauyan wato Mista Olanipekun, wato lauyan Jegede a karar da ya shigar na nuna wanda yake kara a matsayin wanda bai cancanta ba kasancewar bai bi sahihin hanyar da dokar jam'iyar ta tanada ba kafin mutum ya samu damar taka karara a karkashin jam'iyyar

An sauke sunan Jimoh Ibrahim a matsayin dan takarar PDP

Kotu taba hukumar zabe umarnin data gabatar da Jegede a matsayin dan takarar gwamnan jahar Ondo a karkashin jam'iyar PDP.

Haka kuma, kotun daukaka karan ta soke sunan Jimo Ibrahim a matsayin dan takaran gwamna a karkashin jam'iyar PDP a zaben da za'ayi a ranar Asabar.

Haka kuma, alkalin kotun mai suna Justice Saulawa, ya bukaci da hukumar zabe ta soke sunan Jimo Ibrahim ta maida sunan Eyitayo Jegede a matsayin wanda zai taka takaran gwamna a karkashin jam'iyar PDP.

KU KARANTA: An tilasta ma barauniya cin kashinta bayan taci duka

Alokacin da yake yanke hukuncin, Alkali Saulawa, ya bayyana cewar, bayan saurarin kararraki tare da shedun da suka gabata daga wangarorin biyu, kotun ta baiwa hukumar zabe damar data sauke sunan Jimo Ibrahim daga cikin sunan da take dashi a matsayin wanda zai taka takaran gwamna a karkashin jam'iyar PDP a jahar Ondo, ta sanya sunan Mista Jegede a matsayin sahihin dan takaran jam'iyar PDP.

Haka kuma, kotun ta yarda da Mista Olanipekun wato lauyan Mista Jegede na zargin da yayi ma Mista Jimo Ibrahim a matsayin wanda bai cancanta ya taka takara a gwamna a karkashin jam'iyar PDP din ba, saboda cika wasu sharudda na tsayawa takarar gwamnan da jam'iyar ta tanada.

Duk wasu zarge zarge dai a kotun anyima Mista Ibrahim, inda aka bayyana cewar bai bi ka'idar daya kamata ba, inda lauyoyin nasa suka fice daga cikin kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel