Anyi shellan batan sojoji 46 bayan harin Boko Haram

Anyi shellan batan sojoji 46 bayan harin Boko Haram

- Sojojin Najeriya sun sanar da cewa yan uwan wani jami’I da sojoji 45 sunce basu ga masoyan nasu ba

- An bayyana cewa sojojin sun aika da sako ga dukkan inda sojoji suka zama a fadin kasar don sanar dasu cewan ba’a ga sojoji 46 cikin 83 ba bayan harin Boko Haram yan makonni da suka wuce

Anyi shellan batan sojoji 46 bayan harin Boko Haram
Kakakin sojoji Kanal Sani Usman Kukasheka

Sojojin Najeriya sun yi shella cewa ba’a ga sojoji guda 46 ba bayan wani hari da Boko Haram suka kai a tushensu dake Gashigar, jihar Borno kimanin makonni biyar da ya wuce, jaridar Premium Times ta ruwaito.

An bayyana cewa yanzu sojojin sun sanar da yan uwan jami’I daya da kuma sojoji 45 sun kuma bukaci masoyansu da su aika masu da cikakken bayanin asusun magajinsu don ‘biyan kudin da aka aika masu’.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa an tura wani sako dake dauke da dukkan wannan bayanai daga hannun Laftanal Kanal Jimoh, sabon kwamandan dojojin Najeriya 145 dake Damasak, jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Ka koma gonarka dake Daura - Kungiya ga Buhari

Ance ya sanar da dukkan tushen sojoji daga gurin da aka kaddamar da batan sojoji 83 yazo abaya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an tura rundunar da suka bata Gashigar dake jihar Borno a matsayin bangare na ‘Operation Gama Aiki’ da kudirin tarwatsa mafakar yan ta’adda dake kusa da iyakar Najeriya da Nijar da kuma Chadi.

Hukumar Legit.ng ta tuna cewa an rahoto yan ta’addan sun mamaye sansanin a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, sunji ma sojoji 13 rauni sannan kuma suka tafi da sojoji da dama.

Bisa da sanarwan da sojoji sukayi a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, aiki don da dawo da sojojin da suka bata na ci gaba kamar yadda sojojin suka bi sahun kungiyar muslincin da suka kai hari sansanin.

https://youtu.be/gAlXdItITbw

Asali: Legit.ng

Online view pixel