Shugaba Buhari ya isa kasar Equatorial Guinea (HOTUNA)

Shugaba Buhari ya isa kasar Equatorial Guinea (HOTUNA)

A jiya Talata 22 ga watan Nuwamba ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Malabo don halartan taron shuwagabannin kasashen Afirka dana Larabawa.

Shugaba Buhari ya isa kasar Equatorial Guinea (HOTUNA)

Taron na kwanaki biyu zai mayar da hankali ne kan yadda yankunan biyu zasu habbaka harkokin cinikayya, kasuwanci, tare da inganta tattalin arzikin juna don ganin an samar da cigaba mai daurewa musamman kan fannonin sufuri, sadarwa da harkar mai da iskar gas. Bugu da kari taron zai tattauna batun yan gudun hijira da rikcin Boko Haram ya shafa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Equatorial Guinea

Shugaba Buhari ya isa kasar Equatorial Guinea (HOTUNA)

Shugaba Buhari ya samu tarba na karamci daga jami’an kasar Equatorial Guinea, kamar yadda wata sanarwa ta bakin mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina ta bayyana “taron da zai samu halartan shugabannin kasashen Afirka dana Larabawa, ana sa ran zai tabbatar da yarjejeniyar Malabo tare da samar da hanyoyin habbaka cinikayya da kasuwanci tsakanin yankunan biyu daga 2017-2019.

Shugaba Buhari ya isa kasar Equatorial Guinea (HOTUNA)
Shugaba Buhari kafin tafiyarsa

“Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo gida a ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba, sa’annan shugaba Buhari zai yi wata ganawa ta musamman da shugabannin kasashen Larabawa don sake duba ga yarjejeniya daban daban da aka cimmawa tsakanin kasashen da Najeriya don inganta su, musamman wadanda suka shafi harkar noman da samar da ababen more rayuwa.”

Zaku iya bin kadin labaran mu shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel