An yanke ma mutane 3 hukuncin kisa domin kashe Afolabi

An yanke ma mutane 3 hukuncin kisa domin kashe Afolabi

- An yanke ma mutane 3 hukuncin kisa dalilin kisan wani Suleiman Afolabi ranar Kirsimati

- Sunce danuwan mamacin ne ya kaimasu hari da kuam mai shari'ar tayi watsi da kalamansu kafin ta yanke hukunci

An yanke ma mutane 3 hukuncin kisa domin kashe Afolabi

An yanke ma Ibrahim Omilade dan wani basaraken gargajiya a Lagos, basarake Bashiru Omilade hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan kisan da aka yima wani Suleiman Afolabi yayin da suke fada ranar Kirsimatin 2012.

The Nation ta ruwaito cewa 'yanuwa biyu, Shola da Kayode Oni suma an yanke masu hukuncin kisa kan wannan laifin. An ce kisan Suleiman ya faru a titin Eyin Ogun , Mafoluku a Oshodi inda aka ce an sassare shi da adda.

KU KARANTA: Ba daga siyasa ba? Karanta inda Saraki yace ya samu kashi 95% na dukiyar sa

Mai shari'a Kudirat Jose ta babbar kotun kasa dake Ikeja, Lagos ta zartar da hukuncin kisa kan mutanen ukku bayan ta same su da laifin kulli da kuma kisan kai da masu gabatar da kara mista Babatunde Ogungemowo da mista Olarewaju Ajanaku suka yi masu.

Tace: “Na sami wadanda ake kara da laifi kamar yadda aka tuhumce su kan laifin kisa da hadin kai kuma za'a kashe su ta hanyar ratayewa har sai sun mutu.

Ta bada shawara ga matasa dasu yi kokarin samun masalaha kan ban-bance ban- bancensu ba tare da amfani da mummunan karfi ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel