Rashin kunya ne gwamnatin PMB ta rika yin maganar 2019

Rashin kunya ne gwamnatin PMB ta rika yin maganar 2019

Tsohon dan majalisa dokta Junaid Mohammed ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin maras kunya saboda tana cewa 'yan Najeriya zasu goyi bayansa a 2019.

Rashin kunya ne gwamnatin PMB ta rika yin maganar 2019

Mohammed yace gwamnatin Buhari na kwadan mulki, yaudara da cin rashawa har ta fara yin maganar 2019 bayan babu abinda tayi cikin shekara daya da rabi kan mulki.

Dokta Junaid Mohammed wani tsohon dan majalisar wakilai a jamhuriya ta biyu ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin maras kunya domin tana cewa 'yan Najeriya zasu koma bayan shugaban a shekara ta 2019,  Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Ku kuka jawo wa kanku bala’in da kuke ciki; Sakon APC zuwa ga PDP

In an tuna, ranar Litinin, 21 ga Nuwamba, fadar shugaban kasar tayi watsi da labarun da ake yi cewa talakawa zasu kaurace ma shugaba Muhammadu Buhari a 2019, inda take cewa maganar bata da asali kuma abin ban dariya ce.

Ba tare da bata lokaci ba, ranar Talata 22 Nuwamba, Mohammed yace rashin kunya ne gwamnatin Buhari ta rika yin maganar 2019 duk da babu wani abin azo a gani da tayi bayan shekara daya da rabi bisa mulki.

Mohammed yace: “Abin ban takaici ne kuma abin ban kunya cewa gwamnatin da ba tayi komai ba ta fara maganar 2019. Abin ban takaici ne jam'iyya kamar APC wadda ta fara rugujewa tana maganar 2019 bayan babu abinda zasu gwada ma 'Yan Najeriya a shekaru hudu da aka basu. Wannan sheda ce cewa kwadan mulki suke ga kuma yaudara da cin rashawa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel