Mutanen GEJ na goyon bayan Oke yayin da AD ke zargin PMB

Mutanen GEJ na goyon bayan Oke yayin da AD ke zargin PMB

- Ana cewa tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan Neja Delta kuma shugaban shirin afuwa na shugaban kasa, Onorabul Kingley Kuku na bada goyon baya ga basarake Olusola Oke na Alliance for Democracy (AD)

- Ana zargin shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyya mai mulki ta All Progressive Congress (APC) da yima mambobin AD barazana gabannin zaben gwamnan jihar Ondo da za'a yi ranar Assabar

Ana cewa tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan Neja Delta kuma shugaban shirin afuwa na shugaban kasa onorabul Kingsley Kuku ya bada goyon baya ga burin basarake Olusola Oke na Alliance for Democracy (AD)

Kuku, wanda mamba ne na PDP ya nisanta kansa daga bangarorin na PDP, ana kuma cewa yana daya daga cikin wadanda suka matsa ma Oke ya koma AD bayan kayen daya sha a zaben fidda gwani da aka yi ranar 3 ga Satumba.

KU KARANTA: Ku kuka jawo wa kanku bala’in da kuke ciki; Sakon APC zuwa ga PDP

Har ma an fara cika garin Ese-Odo da hotunan Oke da Kuku 'yan kwanaki kafin zaben wadanda ke dauke da rubutun dake cewa "Ubangiji na farin cikin cika alkawarinsa. Har yau ina tare da kai".

Rohoton na kuma cewa mista Kuku ya bayar da babbar gudummuwa wajen takarar gwamna da Oke yayi a 2012 lokacin da yayi takara da gwamna Olisegun Mimiko na jam'iyyar Labour da Oluwarotimi Akeredolu na Action Congress of Nigeria (ACN) a lokacin, yanzu Akeredolu zai yi takara kalkashin All Progressive Congress (APC).

A biyo mu shafin sada zumunta @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel