Kakakin majalisar Imo na fuskantar tsigewa

Kakakin majalisar Imo na fuskantar tsigewa

Akwai bacin rai da yawa a majalisar jihar Imo kan zargin da ake ma kakakin majalisar na burin zama gwamna a inda ake cewa na kawo cikas ga ayyukan majalisar.

Kakakin majalisar Imo na fuskantar tsigewa
Speaker Acho Ihim faceing impeachment over his governorship ambition

Kakakin, Acho Ihim, wanda kuma shine shugaban kungiyar majalisun kasashe renen Britaniya reshen Afrika kuma tsige shi ba zai zama alfanu ba.

Dalilin ana masa zargin kwadayin kujerar gwamnan jiharsa, za'a tsige kakakin majalisar jihaf Imo Achi Ihim. Abokan aikinsa sun bukaci daya aje mukaminsa koko su tsige shi. Ihim, a halin yanzu shine shugaban kungiyar majalisun kasashe renon Britaniya sashen Afrika.

KU KARANTA: YANZU-YANZU: ‎Anyi rashin rayuka 11 a rikicin ‘yan sanda da mafarauta

Daily Sun ta ruwaito cewa wasu 'yan majalisa na zargin kakakin da maida majalisar tamkar wani bangare na fadar gwamnatin jihar dalilin burinsa na zama gwamna. Bayan wani taro da akayi a gidan wani babban dan siyasa a jihar, 'yan majalisar sun dau alwashin tsige kakakin idan bai aje mukaminsa ba.

Rohoton ya ambato wani dan majalisa na cewa:

"Abubuwa basu taba lalacewa kamar haka ba a jihar inda 'yan majalisa basu da wani mutunci a idanun jama'a dalilin burin kakakin majalisa wanda ya maida kansa tankar mai yima gwamna aiki. Domin yana son zama gwamna a 2019, yana yima ikon majalksar zagon kasa yadda ta kai ba'a biyan mambobi alawus dinsu."

A nashi maida martanin, mai magana da yawun kakakin, Ben Ilochuonwu, yayi watsi da maganar tsige ubangidansa. Ya kuma karyata zargin da akeyi cewa kakakin nada burin ya gaji gwamna Rochas Okorocha a 2019, yana mai cewa kakakin da 'yan majalisar nada jituwa na tsawon wani lokaci.

A biyomu a shafinmu na tuwita @naijcomhausa

Kakakin majalisar Imo na fuskantar tsigewa
Kakakin majalisar

Asali: Legit.ng

Online view pixel