Babu kudi a bangaren kiwon lafiya- Adewole
- Najeriya ta zama abin dariya a idon duniya
- Wanna ya faru ne sanadiyar rashin kudi a bangaren ilimi
- Wanna shine Maganan ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewale

Ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewole. A 22 ga watan Nuwamba yace rashin bayar da kudi ga ma’aikatar koiwon lafiya ya sanya Najeriya ta zama abin dariya a idon duniya. Kuma yace da alamun wannan kalubalen zai cigaba.
KU KARANTA: Orji Uzor Kalu dukiyar siyasa ne – Gwamna Okorocha
Adewole yayi wannan bayani ne a wata taron da majalisar wakilan tarayya ta shirya akan ayyukan kiwon lafiya.
Yace: “Mun zama abin daniya a idon duniya lokacin da aka rage kudin kasafin kudin kasa na 2016 da kasha 33 cikin dari. Maganan shine wannan ba kasa bace wacce ta shirya yin aiki.”
Gwamnatin shugaba Buhari ya baiwa bangaren kiwon lafiyan kudi N221.7billion a kasafin kudin 2016, kasa da kudi N259.7bn da Goodluck Jonathan yake badawa.
A biyo mu @naijcomhausa
Asali: Legit.ng