Rundunar sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta

Rundunar sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta

Rundunar sojin samar Najeriya ta kai wata mumunan hari ga yan tasa kayar bayan Boko Haram a jihar Borno.

Rundunar sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta

A wata jawabin da ta daura a shafin ta na sada raáyi da zumunta, rundunar sojin samar  ta tabbtar da labarin yadda sukayi amfani da jirgin sama wajen tarwatsa wasu yan boko haram inda suka ganawa a ranar laraba, 16 ga watan Nuwamba.

An kasha wasu yan taáddan kuma wasu sun arce.

KU KARANTA: Reno Omokri ya aika da sako zuwa ga Buhari da Jonathan

Karanta jawabin:

“Rundunar sojin samar Najeriya sun kai wasu hare-hare sassan an Boko Haram inda suka kasha yan taáddan da dama. A rana 16 ga watan Nuwama, wata naúran liken asiri ta bada rahoton wata mabuyan yan boko haram karkashin wata bisihiya a Kadari.

“A ranan 18 ga watan Nuwamba, jirgin rundunar sojin sana ta kai wata hari inda ta hallaka yan taáddan da dama kuma wasu sun arce a Ngoshe."

A makon da ya gabata, runduna sojin kasa sun kai wata inda aka hallaka yan boko haram guda 11.

A jawabin da kakakin sojoji Kanal Kukasheka ya bayar, yace rundunar sojin 119 batallion sun shiga kauyen Kangarwa inda suka shiga musanya wuta da yan taáddan.

ku biyo mu a shafin Tuwita :@naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel