Dalilin daya sa ya wajaba FG ta duba bukatun mutanen Ogoni

Dalilin daya sa ya wajaba FG ta duba bukatun mutanen Ogoni

- Basarake Goddy Nwikpo, jigo ne a kasar Ogoni. Shugaba ne na hukumar masarautar alummarsa dake karamar hukumar Khana, Ogoni a cikin jihar Rivers

- A wannan hirar da yayi da Austin Oyibode na Legit.ng yayi magana kan abubuwan dake damun mutanen Ogoni, fatarsu da kuma kiran da suke ma gwamnatin tarayya data cika alkawarinta na tsaftace kasar Ogoni

Gaya mana game da kasar Ogoni: Tarihin Ogoni ya kasu gida biyu. Daya na cewa mun zo daga Ghana, yayin da daya ke cewa munzo daga jihar Akwa Ibom.

Amma wanda yake a rubuce shine wanda ke cewa daga Ghana muka zo a matsayin masunta, kuma a matsayin mu na bakin masunta mun ci gaba da yin su har muka kai Bonny. Suna kiran mu baki tamkar wadanda ba zasu zauna tare dasu ba,sai suka tura mu cikin kasar. Da muka shiga cikin kasar muka kafa helkwatar mutanen Ogoni ta gargajiya. Idan kana bukatar sarautar gargajiya ko wani abu mai muhimmanci a kasar Ogoni, to dole ne kaje wurin domin neman izini (Nama).

KU KARANTA: Abdulmumin Jibrin zai nemi takarar shugaban kasa a 2019

Gaya mana halin rayuwa a kasar Ogoni bayan lalata wurin da aka yi: Rayuwa bata canza ba, dalili shine dibar mai ya lalata wurin. Ya lalata gonaki da koguna. Nan ne rayuwar mu take, kamun kifi, sakar tabarmi,amma halin yanzu babu abinda zai iya rayuwa da barnar da aka yima muhalli. Ruwa baya shawo domin duk ruwan da ka diba sai kaga mai a sama. Saboda haka bamu da ruwa, ruwan da muke dashi na borehole ne. In kana bukatar ruwa mai kyawu sai kayi gina mai zurfi, kuma bamu da kayan ginin.

Akwai kampanonin mai masu aiki a wurin, me suka yima al'ummar dake wurin? A yanzu babu kampanonin mai a kasar Ogoni. Ni na rubuta wasiku ga Shell, Chevron da NNPC, su ke aiki a kasar Ogoni a lokacin. Na aika masu da wasikun ranar 22 ga Disamba 1992 lokacin da nike sakataren kungiyar rayuwar mutanen Ogoni. Mun basu kwanaki 21 su duba bukatunmu amma da basu maido da amsa ba, ranar 4 ga Janairu 1995 sai muka kore su domin rashin duba bukatunmu.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel