Orji Uzor Kalu dukiyar siyasa ne - Gwamna Okorocha

Orji Uzor Kalu dukiyar siyasa ne - Gwamna Okorocha

- Gwamna Rochas Okorocha ya bayyana tsohon gwamnan jihar Abiya basarake Orji Uzor Kalu a matsayin arziki a siyasance bayan ya canza sheka zuwa APC

- Gwamnan jihar Imo ya bayyana canjin shekar Kalu a matsayin ci gaba ba wai na APC kawai ba, har ma na yankin kudu maso gabashin kasar

- PPA ta Abia tace matakin da Kalu ya dauka yayi ne domin tsira da mutuncinsa domin an riga an kore shi daga jam'iyyar

Orji Uzor Kalu dukiyar siyasa ne - Gwamna Okorocha
Governor Rochas Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bayyana tsohon gwamnan jihar Abiya basarake Orji Uzor Kalu a matsayin arziki a siyasance, cewar rohoton The Punch.

A cewar Okorocha, canjin shekar Kalu zuwa All Progressive Congress ci gaba ne ba ga jam'iyyar kawai ba har ma ga yankin kudu maso gabas.

KU KARANTA: Abdulmumin Jibrin zai nemi takarar shugaban kasa a 2019

Okorocha ya fadi haka ranar Litinin 21 ga Nuwamba a Owerri ta wata sanarwa da sakataren watsa labaransa Sam Onwuemeodo ya bayar. Sanarwar na cewa:

"Orji Kalu, gawurtaccen dan Igbo ne kuma arziki ne wanda kowace jam'iyyar siyasa zata so ace yana tare da ita. Idan aka sami mutane irin su Orji Uzor Kalu na haduwa dani a APC, zamu kawo ci gaban kasar Igbo kalkashin APC jam'iyyar dake mulki."

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel