Reno Omokri ya aika da sako zuwa ga Buhari da Jonathan

Reno Omokri ya aika da sako zuwa ga Buhari da Jonathan

Daga Edita cewa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda yayi bikin cika shekaru 59 ranar 20 ga Nuwamba wanda Muhammadu  Buhari ya kayar a zaben shugaban kasa da akayi shekarar data wuce. Shugaban mai ci ya kan dora laifi kan gwamnatin data shude na dukkan matsalolin kasar.

Reno Omokri wani kakakin tsohon shugaban ya rubuta ma shugabannin biyu sako yana basu shawara da su hada kai domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta.

KU KARANTA: Mu zamu zabi shugaban kwamitin amintattu– Gwamnonin APC

Zuwa ga shugabannina:

Yadda zaka gane mai biyayya, sai ka janye karuwa da yake yi da kai. Idan biyayyar ta ragu to kasan ta karuwar da yake yi da kai ne, ba kai yake ma biyayyar ba. Ya kamata shugaba Buhari ya dauki darasi daga tsohon shugaba Jonathan. Dubi mutanen daya nada, jakadu wadanda suka yi ikrarin matukar kauna ga shugaba Jonathan .

Nawa ne daga cikinsu suka tuna cewa jiya ne ranar haifuwarsa? Ka kula da wadanda kake kullin siyasa dasu wadanda ke maka rawa suna maka karya cewa dokta Jonathan ya jawo maka matsalolin ka, 'yan baranda ne ba abokai ba.

Kada ka dauki dan baranda tamkar aboki, ka jira sai ranar tuna haifuwarka ta farko ta zagayo bayan ka bar mulki kafin ka san abokanka na gaskiya.

Ra'ayin da aka bayyana a wannan kasidar ra'ayin marubucin ne, kuma ba dole ra'ayin editan  Legit.ng bane.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel