Gwamnonin kudu maso yamma na taron tattalin arziki

Gwamnonin kudu maso yamma na taron tattalin arziki

Akinwunmi Ambode na Lagos, gwamna Rauf Aregbesola  na Osun da gwamna Ayodele Fayose  na Ekiti ne suka halarta

Gwamnonin kudu maso yamma na taron tattalin arziki

Gwamnonin kudu maso yamma  na kokarin yin gangami domin tattauna maganar kudi da kuma yadda ya shafi yankin a lokacin da ake ciki na tattalin arziki mai sarkakkiya

An yi taron tattalin arzikin a garin Ibadan ta jihar Oyo ranar Litinin 21 ga Nuwamba wanda gwamna Abiola Ajimobi ya dauki bakunci.

KU KARANTA: Za’a rika ba mata masu ciki tukwuici a wadannan jihohin 10 na Arewa (Karanta)

Wadanda suka halarci taron sun hada da Akinwunmi Ambode na Lagos, gwamna Rauf Aregbesola  na Osun da gwamna Ayodele Fayose  na Ekiti. Gwamna Olusegun Mimiko bai sami halarta ba amma ya sami wakilcin sakataren gwamnatin jihar mista Rotimi Adelola.

Gwamnonin sun aje banbancin siyasa domin tattauna yadda kudu maso yamma zata sami ci gaba a fannin tattalin arziki.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel