An kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su

An kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su

- Yayinda yake jawabi a Abuja ministan birnin Malam Muhammad Musa Bello ya fada cewa rundunar hadin gwuiwar jami'an tsaro ta kubutar da mutane goman da aka sace a karamar hukumar Kuje.

- Kakakin ministan Abuja Abubakar Sani yace ministan ya sanarda duniya dangane da gagarumar nasarar da aka samu wajen kubutar da mutanen da aka sace aka kuma yi garkuwa dasu makon jiya.

An kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su
Police arrest suspected kidnappers
An kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su
The suspects

Kakakin ministan yace basu biya kudin fansa ba saboda gagarumin shirin da jami'an tsaro suka yi. Injishi jami'an tsaron sun kewaye inda wadanda suka yi garkuwa da mutanen suke fakewa. Daga nan ne suka yiwa bata garin diran mikiya.

KU KARANTA: INEC ta watsa wa PDP kasa a ido

Shi ministan na Abuja yace a daidai lokacin da ake kokarin kubutar da mutanen wani jami'in tsaron farin kaya ya rasa ransa sakamakon rashin lafiya da ya samu.

Saidai yayinda ake farin cikin kubutar da mutanen sai gashi an sake sace wasu yara uku a karamar hukumar Kuje din. Umar Suleiman na cikin wadanda abun ya shafa domin an sace 'yarsa yar shekara biyu.

 

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel