Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin

Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin

Jaridar NAIJcom ta tattaro muku Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin 21 ga watan nuwamba,2016

1. YANZU-YANZU: FG ta gurfanar da alakalin kotun koli Ngwuta

Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin
Justice Sylvester Ngwuta

An gurfanar da alkalin kotun koli mai shari'a Sylvester Ngwuta gaban wata babbar kotun kasa dake Abuja ranar Litinin 21 ga Nuwamba

2. Senata Yele Omogunwa na jihar Ondo ya sheke APC

Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin

Jam’iyyar Peoples Democratic PartyPDP ta shiga cikin rudu yayinda Senata Yele Omogunwa na jihar Ondo ya sheke APC daga PDP.

3. Kada a sake a daga zaben jihar Ondo - APC ga INEC

Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin

Jam’iyar All Progressives Congress (APC) ta siffanta bukatan jam’iyyar PDP ga hukumar gudanar da zabe ta kasa ai zaman kanta INEC na daga zaben jihar Ondo da aka shirya ranan 26 ga watan Nuwamba.

4. Sabon salon damfara: wata mata ta damfari fasto

Wata mata mai suna, Mary Onu da ‘yar ta Alice sun gurfana gaban wata kotun majitare a jihar Legas da laifin damfarar wani mai kamfanin mota da kuma fasto.

5. Fadar shugaban kasa ta daga shirin daukan maáikata 200,000 zuwa Disamba

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa ta daga shirin da mako daya a wata jawabin ds Legit.ng ta samu a ranan lahadi,20 ga watan Nuwamba wanda mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya sanya hannu.

6. Daga karshe: Buhari yayi magana a Fulani Makiyaya

Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin

Shugaba Buhari ya daura laifin rikicin makiyaya a fadin kasa akan sajewan da wasu yan kasan Libya da Mali sukayi da su.

7. Zahra Buhari zata  auri ‘dan hamshakin attajiri

Muhimman batutuwan da suka yadu a jiya litinin

Zahra Buhari daya daga cikin ‘yaya matan shugaba MUhammadu Buhari ,wacce ta karashe karatun jamíar ta a kasan Ingila tana shirin shiga dakin mijinta.

8. Ba zan taba raina Tinubu ba - Fayemi

Ministan maádinai, Dr Kayode Fayemi,yayi watsi da wasu maganganun da ke yaduwa kwanankin nan cewa “Tinubu shugaba ne wanda shine sanadiyar matsalolin sa”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel