Gwamnoni da ka iya barin APC tare da Tinubu

Gwamnoni da ka iya barin APC tare da Tinubu

Akwai Baraka a Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar nan

Wasu Gwamnoni na shirin barin Jam’iyyar APC

– Wani Jigo a Jam’iyyar ta APC, Bola Tinubu bai jin dadin abin da yake faruwa

Gwamnoni da ka iya barin APC tare da Tinubu

Bayanai daga Jaridar New Telegraph na nuna cewa wasu daga cikin Gwamnonin Jam’iyyar APC na shirin barin Jam’iyyar nan da zuwa zaben 2019. Wani babban Jigo a Jam’iyyar ta APC, Bola Tinubu bai jin dadin abin da yake faruwa a harkar siyasar kasar.

Jaridar tace mafi yawan gwamnonin da ake tunani za su iya ficewa daga Jam’iyyar ta APC, Gwamnonin Kasar yarbawa ne da kuma Arewa-ta-Tsakiya. Watakila magoya bayan Bola Tinubu, su janye jiki su kafa ta su Jam’iyyar.

KU KARANTA: Buhari ba zai kai labari ba-PDP

Ga wasu daga cikin wadannan Gwamnoni:

Rauf Aregbosola

Aregbosola yanzu ya shekara 6 yana rike Gwamna a Jihar ta Osun. Gwamnan Jihar Osun na tare da Bola Tinubu. Yana daga cikin masu iya ballewa.

Akinwumi Ambode

Gwamnan Jihar Legas Ambode shi ma na hannun daman Tinubu ne. Yah au mulki a zaben bara, yana kuma iya barin APC.

El-Rufai

Malam Nasir El-Rufai, tsohon Minista ne, kuma Gwamnan Jihar Kaduna na iya canza sheka daga APC kafin zabe mai zuwa.

Aminu Tambuwal

Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal na iya barin APC idan har Bola Tinubu ya bude sabuwar Jam’iyya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel