Dubun wani sojan bogi a Najeriya ta cika

Dubun wani sojan bogi a Najeriya ta cika

Rundunar 33 Artillery Brigade ta sojojin Najeriya dake jihar Bauchi ta kama wani sojan bogi mai suna Adamu Alexander mai shekaru 22 dan asalin garin Maiduhguri dake jihar Borno.

Kamar yadda mukadashin daraktan yada labarai na rundunar sojojin, Kyaftin Sunday Akinkunmi ya bayyana, an kama Alexander ne a cibiyar sayar da wayoyi dake cikin garin Bauchi a wata ranar Juma'a da ta gabata, a lokacin da yake kokarin saida wata wayar sata kirar Samsung Galaxy Note 5 kan farashi naira dubu saba'in.

Dubun wani sojan bogi a Najeriya ta cika
Dubun wani sojan bogi a Najeriya ta cika
Fake
Dubun wani sojan bogi a Najeriya ta cika
Sojan gona

Kyaftin Akinkunmi ya kara da cewa an kama matsahin ne a cikin kasuwar ta Wunti sanye da kakin sojoji. Sannan kuma an gano cewa farashin wayar da matashin yake kokarin sayarwa ya kai naira dubu 250, inda shi kuma yake kokarin sayar da ita kan naira dubu 70. Haka kuma Alexendre ya shiga hannu ne bayan da sojojin suka samu labarinsa.

Ku Karanta: An gano wadda tafi kowa tsufa a Najeriya (Hotuna)

A wani labarin kuma a Najeriyar, rundunar sojin kasar ta musanta cewa ta rage yawan sojojinta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rundunar sojin na mayar da martani ne akan fargabar da wasu mazauna birnin Maiduguri ke yi cewa, karuwar hare-haren kunar bakin wake daga 'yan kungiyar Boko Haram yasa gwiwar su ta yi sanyi.

A wata hira da majiyar mu tayi da wasu mazauna birnin Maiduguri sun bayyana cewa matakin rage sojojin ya taimaka wajen karuwar hare-hare kunar bakin wake da ake fuskanta a jihar tare da haifar da fargaba.

Sai dai kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria Kanar Sani Usman Kukah Sheka ya ce bai kamata ba wasu jama'a su rika cewa ana cikin fargaba a birnin Maiduguri, inda ya nanata cewa sojojin kasar sun karya lagon Boko Haram.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel