Guardiola yayi da na sanin ajiye Yaya Toure a benci

Guardiola yayi da na sanin ajiye Yaya Toure a benci

Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola ya tabbatar da yin da na saninsa ajiye dan wasan tsakiya na kasar Ivory Coast Yaya Toure daga cikin yan wasan sa har na tsawon watanni uku da yayi.

Guardiola yayi da na sanin ajiye Yaya Toure a benci

Guardiola ya amsa laifinsa inda, yace amma kuskure ne, musamamman ganin yadda dan wasan ya taka leda a wasan sa na farko tun da aka fara kakar wasa ta bana, ranar 19 ga watan Nuwamba inda ya zura kwallaye biyu da suka baiwa kungiyar Man City nasara.

Tun da fara kakar bana ne wani rikici ya kunno kai tsakanin Guardiola da Yaya Toure, wanda hakan ya sanya Guardiola ajiye Yaya daga taka leda a kungiyar. Sa ga shi a ranar Asabar 19 ga watan Nuwamba Guardiola ya ba Yaya daman buga wasan sa na farko, inda shi kuma Yayan bai yi kasa a gwiwa ba, sai daya jefa kwallaye 2 a zaren abokan karawarsu Crystal Palace.

KU KARANTA: An nada sabon Kwamandan Soji a yankin Neja Delta

Duk da haka Yaya Toure ba zai samu buga wasan Man City da Borussia Monchengladbach ba, dayake Guardiola bai yi rajistan sa ba cikin jerin yan wasan da zasu buga ma kungiyar wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai.

A yanzu dai Guardiola ya amsa laifinsa, inda yace yayi kuskuren rashin rajistan Yaya Toure cikin jerin yan wasan da zasu fafata ma kungiyar a gasar cin kofin nahiyar Turai.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel