INEC ta yi watsi da bukatar PDP

INEC ta yi watsi da bukatar PDP

- Hukumar Zabe a Najeriya taki amincewa da bukatar Jam’iyyar PDP na dage zaben Gwamnan Jihar Ondo da ake shirin yi a karshen wannan mako

- Jam’iyar PDP ta bukaci dage zaben ne dan bai wa kotun koli damar yanke hukunci kan ta kaddamar tsayar da dan takara

INEC ta yi watsi da bukatar PDP
The Independent National Electoral Commission (INEC) is under pressure to shift the Ondo polls.

Hukumar zaben tace Jam’iyyu 28 suka tsayar da ‘Yan takara a zaben, saboda haka ba za ta dage zaben ba saboda bukatar Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Tinubu da Buhari sun raba gari game da zaben Ondo

A ranar 26 ga wannan watan na Nuwamba za a gudanar da zaben.

Mai karatu zai iya tunawa cewar jam’iyyar PDP da ke adawa a Najeriya ta bukci hukumar Zabe ta dage zaben gwamnan Jihar Ondo da za a gudanar a ranar 26 ga wannan watan nan Nuwamba har sai kotu ta tabbatar da dan takarar jam’iyyar tsakanin Eyitayo Jegede da Jimoh Ibrahim.

PDP ta nemi dage zaben ne saboda rikicin Jam’iyyar inda mutane biyu ke ikirarin zama ‘Yan takara gwamnan Jihar ta Ondo.

Wannan kuma na zuwa ne bayan kotun daukaka kara a Abuja ta dage zartar da hukunci akan koken da Eyitayo Jegede ya shigar na tabbatar da shi a matsayin dan takarar gwamna sabaniin Jimoh Ibrahim da kotun Tarayya ta tabbatar a matsayin dan takarar gwammnan na PDP.

Jimoh Ibrahim dai na bangaren shugabancin Senata Ali Modu Sheriff, yayin da Jegede ke bangaren Senata Ahmed Makarfi da ke hamayya da Sherif a shugabancin Jam’iyyar na kasa.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel