Uba ya tsine ma dan sa a tallar jarida

Uba ya tsine ma dan sa a tallar jarida

Wani fusattacen uba ya zabi hanya mai ban al’ajabi na yafe ma duniya dan sa mai shekaru 39.

Mtumin da aka kira da Mista Andrew Chukwurah Nworah, ya nemi wani bangare a takardan jarida, don fada ma duniya dalilinsa na yafe ma duniya magidancin dan sa.

A cewar Mista Nworah, dan sa mai shekaru 39 mai suna Bethel Ogechukwu Nworah na barazana ga rayuwarsa. Ya kuma zarge shi da rashin ladabi, ya kara da cewa karda a bari ya gaji dkikoyinsa idan ya mutu, haka kuma kada a bari ya je binne sa a ko wani hali.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya roki yan bindigan Niger Delta

Kalli hoton tallar jaridar a kasa:

Uba ya tsine ma dan sa a tallar jarida

Ya rubuta:

“Ni Mista Andrew Chkwurah Nworah dake kauyen Akwa Ifitedun na karamar hkumar Dunukofia dake jihar Anambra Najeriya, na yafe ma duniya da na Mista Bethel Ogechukwu Nworah, mai shekaru 39, saboda rashin ladabinsa da kma barazana ga rayuwata.

Don haka Mista Bethel Nworah ba zai kasance a gurin jana’izata ba idan na mutu. Kuma karda ya gaji komai daga cikin dukiyata a Ifitedunu da ko ina, kuma karda a bari ya ga wasiyata.

Duk wanda yayi ko wani kasuwanci tare da Bethel Nworah da sunana, ba da yawu na ba kuma shi zai dauki alhakin abunda zai je ya dawo, jama’a ku lura”

Allah ya kyauta! Wa ka fi tasayi cikin su? Uba ko da?

Asali: Legit.ng

Online view pixel