An kai hari gidan Mamman Daura a Kaduna

An kai hari gidan Mamman Daura a Kaduna

- ‘Yan bindiga sun sace wani tsohon ministan Najeriya jiya a garin Kaduna

- Wasu ‘yan bindiga ne suka yi gaba da Ambasada Bagudu Hirse

An kai wannan hari ne a gidan Mamman Daura da ke garin Kaduna

An kai hari gidan Mamman Daura a Kaduna
Mamman Daura

 

 

 

 

 

 

 

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sace wani Tsohon Ministan Kasar nan a Gidan Alhaji Mamman Daura da ke Garin Kaduna. Wasu ‘Yan bindiga ne dai da ba a san su ba, suka sace Tsohon Ministan harkokin waje na Kasar, Ambasada Bagudu Hirse.

Wannan abu ya faru ne dai jiya a gaban Gidan Alhaji Mamman Daura da ke kan Titin Inuwa Wada a cikin Garin Kaduna. Ana zargin cewa Alhaji Mamman Daura yana gida a lokacin da wannan abu ya faru. An ce ko a lokacin yana karbar ziyara daga ‘Yan uwa da abokan arziki.

KU KARANTA:  Ba na iya barci-Gwamnan Imo

Tsohon Ministan dai ya zo Garin ne domin ta’aziyar rashin Marigayi Ibrahim Dasuki, tsohon Sarkin Musulmi. Gidan Marigayi Dasuki bai da nisa da Gidan Alhaji Mamman Daura, don haka ne Ambasadan ya tsaya don ya gaida Mamman Daura.

Wanda abin ya faru a gaban sa, yace bayan Alhaji Bagudu ya fito daga mota tare da wani abokin sa, sai wasu mutane kwatsam suka keto a guje a mota kirar Toyoto Corollo sun sha damara, Nan-take suka ce ya shiga motar su, ko da ya tsaya wata-wata, sai suka harba bindiga, tuni kowa ya tsere. Yanzu haka dai ba a san inda suka yi da shi ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel