Furucin Hikima da kotabar na Jonathan 10

Furucin Hikima da kotabar na Jonathan 10

A wannan mako ne tsohon shugaba Goodluck Jonathan ke cika sherau 59 da haihuwa, Legit.ng ta kawo mu ku wasu maganganu 10 na hikima da kuma katobara wandanda ba za a manta da su ba a lokacin yana kan karagar mulki

Furucin Hikima da kotabar na Jonathan 10
Jonathan na yanka ket din murnar cikarsa shekaru 59 da haihuwa

1. Yayin da na ke mulkin Najeriya na yi aiki ne don al'ummar gobe ba dan zaben gobe ba. Kuma ba na yin nadamar abin da na yi.

2. Dole ne mutum ya sadaukar da kansa ya yi aiki dan gaba, idan ba haka ba 'ya'yanka da jikoki su sha irin wahalar da ka sha.

3. Farkon fara karatuna, ba ni da takalma, ba ni da jakar makaranta, a hannu na ke rike littattafaina amma ban taba yin kasa a gwiwa ba. Ba motar da za ta kai ni makaranta amma ban taba kasa a gwiwa ba. Ina tafiyar mila- milai a kafa, na tsallaka kogi kullum zuwa makaranta, duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba. Ba mu da wutar lantarki, ba mu da janareta; da fitilar kwai na ke karatu amma ban yi kasa a gwiwa ba. Duk da wadannan matsalolin na kammala makarantar sakandare, na shiga jami'ar Fatakwal yanzu ga shi ina da digirin digirgir.

4. Sun ce mai bada shawara kan tsaron kasa (Sambo Dasuki) ya saci dala biliyan 2 da miliyan 200. Ban yarda wani haka kawai zai iya satar dala biliyan 2 da miliyan 200 ba.

5. Har na gama mulkina, na kan tabbatar ilimi ya samu kaso mafi tsoka a Kasafin kudi ko kuma a kalla ya shiga cikin bangarori masu kaso mafi tsoka saboda  a lokacin na gamsu kuma har ya yanzu na gamsu cewa ba wata kasa da za ta ci gaba da abin da ke karkashin kasa. Ci gabansu na zuwa ne ta hanyar ilimi.

6. Game da maganar cin hanci da rashawa kuwa, kun san batutuwa da dama na gaban kotu kuma ba na so na to katsalandan ga lamarin Shari'a. Amma dai mun kawo canje-canje kuma mun zo da matakai iri-iri da za su hana cin hanci da rashawa a kasarmu ba tare da mun kwarzanta ba.

7. A karkashin mulkina, ba wani dan Najeriya ko guda daya da a ka kai gidan yari saboda ya yi rubutu ko ya ce wani abu a kaina ko gwamnatin da na ke jagoranta. Duk abin da mai suka zai ce a kaina, na kan tabbatar da ya mori 'yancin fadin albarkacin baki da kuma 'yanci bayan fadar albarkacin bakin.

9. Hakika kasarmu Najeriya ta samu ci gaba sosai tun daga ranar da a ka dawo dimokaradiyya a ranar 29 ga watan Mayu shekarar 1999 lokacin da sojoji su ka hakura su ka mika mulki ga zababbiyar gwamnatin dimokaradiyya wanda ya bada dama ga gwamnatin jama'a daga jama'a kuma don jama'a".

10. Mutuwar kowane dan Najeriya a hannun 'yan ta'adda abin bakin ciki ne. Yakar ta'addanci ya rataya a wuyan duk 'yan Najeriya ba sai sojoji ba. Ina kira ga 'yan Najeriya da su dage da addu'ar samun zaman lafiya kuma su goyi bayan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari son gwamnatin na kokari wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel