Mutane 5 da kuma lalacewar Najeriya

Mutane 5 da kuma lalacewar Najeriya

Najeriya ba ta kai inda ya kamata ta kai ba bayan shekaru 56 da samun 'yancin kai kuma wasu mutane ne ke da alhakin tsundumawar kasar cikin matsalolin da ta ke fuskanta.

Mutane 5 da kuma lalacewar Najeriya
Taswirar Najeriya

1. Iyaye

Tarbiyya dai an ce daga gida ta ke farawa kuma duk lokacin da a ka rasa tarbiyya a gida, to al'amura za su lalace. Gazawar iyaye wajen ba wa 'ya'yansu kyakkyawar tarbiyya na daga cikin manyan matsalolin da kasa kamar Najeriya ke fuskanta. Kuma irin yaran da ba su samu kyakkyawar tarbiyya ba, su ke tasowa su addabi al'umma.

2. Malaman makaranta

Malaman makaranta na daya daga cikin masu ba da gudunmawa wajen matsalolin da kasar nan ke fuskanta, domin yawancin dalibai suna karbar karatu ne a wajen malaman da ke amfani da gurguwar dabara wajen koyarwa. Yanayin ingancin ilimin Najeriya babban dalili ne da ya sa kasar har yanzu ke rarrafe a shekaru 56. Yawancin malaman da ke koyarwa ba su cancanta ba, kuma makarantun na cikin mummunan yanayi ta yanda karatu ba zai tafi daidai ba.

3. Masu wa'azin addini

Najeriya a matsayinta na kasar da ta fi kowacce kasa yawan Masallatai da coci-coci da wasu wuraren ibada na wasu addinai a yammacin Afirka, ko ma a duniya baki daya. Wadanda kuma a ke kira da malaman addini, a maimakon su dora mutane kan hanya, sun bige da shedana iri-iri dan samun kudi. Duk da cewa a kan samu coci-coci kusan guda biyar a ko wane layi, hakan bai hana aikata shedanci a kullum ba, kuma babban dalili shi ne masu wa'azin sun daina fadar gaskiya sun koma neman kudi. Matsawar mutum zai bada kudi (sadaka) to ya zama waliyyi ba kuma a addinin kirista kadai hakan ke faruwa ba. Wasu shugabannin addinin kuma su na fifita son kudi fiye da gaskiya.

4. 'Yan sanda/Jami'an tsaro

'Yan sandan Najeriya sun zama wata alama ta cin hanci da rashawa kuma yawancin 'yan Najeriya ba su yarda za a samu adalci daga wajensu ba. Dole ne hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta lalubo hanyar da za ta tsamo kanta daga wannan matsala tun da ta riga ta zama abin kaico ga kasa. Tun da rashawa ta zama babban cikas a hukumar 'yan sandan. Laifuffuka da dama na faruwa ba tare da an bincika ba yayin da 'yan sandan kan kau da kai. Wasu 'yan sanda da a ka kama da wannan laifi su kan ce, suna yin haka ne dalilin rashin albashi mai kyau, da kuma rashin kulawa daga hukumomi. Da yawa daga 'yan sanda kan fadi karya saboda na goro, da a ke ba su, su kunyata kansu da jama'ar Najeriya.

5. 'Yan siyasa

Idan akwai rukunin mutanen da su ke tsunduma Najeriya cikin kazantar da mu ke ciki yanzu, to su ne mutanen da talakawa su ka zabe su don su bauta musu. Maimakon su bautawa kasa iya iyawarsu da zuciya daya, yawancin 'yan siyasar sun mai da ofisoshinsu wajen neman kudi kawai. Su na satar kudi daga lalitar gwamnati su na taimakawa Kansu da iyalansu kadai. 'Yan siyasa sun dade su na yi wa 'yan Najeriya romon baka iri-iri amma in an zabe su ba sa iya cikawa. In har ba a samo hanyar tsaftace al'amuran 'yan siyasa ba, Najeriya za ta ci gaba da gudun gara su na tarar da zago.

Shin haka lamarai yake? Aikoda naka ra'ayin a shafinmu na Facebook ko ta Tuwita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel