Alakar Ciwon baya da Kujera

Alakar Ciwon baya da Kujera

Mutane da yawa da kuka da ciwon baya amma sun kasa gane cewa irin yanayin zaman da kake yi na da alaka da ciwon da ke damuka na baya da kuma wasu gabobi.

Alakar Ciwon baya da Kujera

Shin yanayin aikinka na dogon zama ne? yana da kyau ka yiwa kanka karatun ta natsu da yadda kake zama a wurin aikinka da yadda kake hutawa a kujera, domin hakan na da tasiri a kan bayanka.

Amma abun mamakin shine wadanda ke matukar samun kudi su na zaune gaban naura mai kwakwalwa ko kuma takardu sun kasa kauracewa matsaloli na rashin lafiya.

Shin ko menene dalili? Dalilin ya ta’allaka ne ga irin zaman da ka ke yi! Dan haka idan a kowanne lokaci zama ya zamar maka lallai a cikin aikin ka, to ya kamata ka fara tunani game da sassan jikin ka.

Sakamakon rashin zama daidai, ganinka da bayanka da wuyanka da kuma cinyoyin ka ke shan wahala matuka.

Za ka ga kamar zama a kan kujera ba shi da wata illa a gare ka, to amma yin amanna da hakan ba daidai bane.

Ya kamata ka sabawa da kanka zama a mike ba tare da wani karkacewa ba, hakan zai fi kyau idan ka samu kujerar da ta dace, saboda hakan ma na taka mu muhimiyar rawa.

Idan ka gaji, ka na so kuma ka canja zama, to ba sai ka muskuta ba, mike  kawai ka dan tashi ka dan kewaya na dan lokaci!  Idan kuma ka na so ka huta a kan kujera ne, to ka yi hakan ta yadda ya dace.

Idan kuma babu makari a bayan kujerar ka, hakan zai karawa aikin wahala, saboda bayanka zai yi saurin gajiya, Amma duk da haka kada ka kaucewa ka’idojin zaman.

Idan kuma har ka mai da hankali sosai wajen yadda ka ke zaman ka, to za ka yi kokari wajen kauracewa matsaloli da suka shafi lafiya.

Ka kula da kanka, sannan kuma wannan hoton mai motsi (video) zai kara ma hasken yadda ya kamata ka yi zauna a daidai!

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel