Yan sanda sun dakile harin yan kunar bakin wake a Maiduguri, 2 sun mutu

Yan sanda sun dakile harin yan kunar bakin wake a Maiduguri, 2 sun mutu

Yan kunar bakin wake guda uku da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sunyi yunkurin tayar da babban kotun tarayya a yankin Jidari Polo dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba.

A cewar ga Sahara Reporters, yan kunar bakin waken masuyi nasarar halaka sosai ba kamar yadda yan sandan Najeriya a cocin dake kusa suka yi nasarar kashe yan kunar bakin waken wadanda suka hada da namiji daya da mata biyu kafin su kai ga halama mutane.

Majiyar ta bayyana cewa daya daga cikin yan kunar bakin waken, mace ta cire rigar bama-bamanta sannan kuma ta gudu ta inda jami’an tsaron suke da hannunta a sama, an kuma kamata a raye.

Sannan mai harin ta cire bam dinta wanda ya kashe abokin ta’asarta namiji.

KU KARANTA KUMA: Goodluck Jonathan ya samu gwarzon tarba a Sakkwato

Jami’an yan sanda a jihar sun bayyana wa yan jarida cewa yan kunar bakin waken ne kawai suka mutu a harin.

An kama Yar kunar bakin wake mace wacce ta mika wuya cikin tawagar, an kuma mikata karkashin kulawar sojojin Najeriya.

Kafin sojojin Najeriya su kwato Maiduguri, babban birnin na jihar Borno ya kasance dandalin yan ta’addan Boko Haram.

A lokuta da dama yan Boko Haram sunyi amfani da yan kunar bakin wake mata da yara gurin kai hare-harensu, musamman a lokutan baya, sojojin Najeriya sunyi ma yan kungiyar ta’addan zindir.

Yan sanda sun dakile harin yan kunar bakin wake a Maiduguri, 2 sun mutu
Jami'an tsaro sun dakile harin yan kunar bakin wake a Maiduguri

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel