Atiku ya taka rawar ‘Dab’

Atiku ya taka rawar ‘Dab’

Wasu matasa sun koya ma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wata sabuwar rawar da samari ke yayi mai suna ‘Dab’.

Atiku ya taka rawar ‘Dab’

Atiku ya nuna ma matasan cewar shima fa ya iya rawa inda ya taka rawar ta ‘Dab’ yayin da ake kaddamar da sabuwar makarantar koyan karatun shari’a na jami’ar ABTI dake Yola a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya daura bidiyon rawar tasa ne a shafinsa na Twitter: ga yadda rawar ta kasance.

 

A wani labari kuma, kungiyar matasan jam’iyyar PDP (PDPNYF) ta bayyana Gwamna Nasir El-Rufai a matsayin maci amana. Kungiyar tayi raddi ne dangane da rikicin daya kunno kai tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna El-Rufai, inda suka ce ai Atiku ne yayi sanadiyyar kasancewar El-Rufai shugaban BPE da zamansa Minista.

KU KARANTA:Yadda Obasanjo yaso ya cigaba da mulki har abada - Atiku

Idan ba’a manta ba Atiku Abubakar ne ya fara bayyana cewar Malam Nasir El-Rufai da Nuhu Ribadu sun ci amanarsa, a wani hira da yayi da jaridar EFCC. Sai dai Gwamna El-Rufai yayi watsi da zantukan Atiku, inda yace alhaki ne kawai ke damun Atiku.

Sai dai kungiyar Matasan ta daura wani hoton El-Rufai yana gaisawa da Atiku a tsugune.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel