Anyi ma wani barawo dukan kawo wuka a Fatakwal

Anyi ma wani barawo dukan kawo wuka a Fatakwal

Dubun wani barawo daya kware wajen sace batiran motocin mutane ta cika yayin da aka kama shi a Unguwar Rumumasi dake garin Fatakwal, jihar Ribas.

Anyi ma wani barawo dukan kawo wuka a Fatakwal

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na dare yayin da barawon ke kokarin balle kofar wata mota, inda abokin aikinsa ke mai gadi.

Sai dai zakara ya baiwa abokin barawon sa’a, inda ya ranta ana kare bayan da jama’an unguwar, tare da masu gadi suka far musu, amma fa shi shugaban barayin bai sha ba, inda yaci dukan tsiya a hannun jama’an bayan sunyi carafken cafke sa.

Anyi ma wani barawo dukan kawo wuka a Fatakwal
Motar da barawon yayi kokarin satan batirinta

KU KARANTA: Inyamurai Uku yan gida daya sun karbi Musulunci a jihar Imo

Nan fa suka mai wani mummunan dauri a jikin wata palwaya, kamar wata naman daji! Daga bisani ne, bayan ya sha ‘tambaya’ barawon ya amsa laifukansa, ciki har da na wata tsohuwa da yayi ma fashi.

Anyi ma wani barawo dukan kawo wuka a Fatakwal

Bayan wani dan lokaci yana cin na jaki, sai jama’a suka mika shi ga jami’an yansanda.

Wannan labarin ya fito ne daga wani ma’abocin karanta labaran Legit.ng, kai ma zaka iya turo mana labarai ko ra’ayoyinka tare da hotuna ta adireshin mu info@naij.com.  Haka nan za’a iya samun mu a shafukan yana kamar su Facebook da Twitter don tsokaci ko korafi.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel