Jonathan ya bayar da ayyukan bogi - Fadar shugaban kasa

Jonathan ya bayar da ayyukan bogi - Fadar shugaban kasa

- Garba Shehu yayi Kira ga shugabannin Neja Delta suyi maganin tsageranci a yankin

- Yace Jonathan bai bayar da kudi domin wasu ayyuka daya bayar ba

- Kakakin shugaban kasar yace sabuwar gwamnati zata maida hankali kan tattalin arziki

Jonathan ya bayar da ayyukan bogi - Fadar shugaban kasa
Garba Shehu

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayar da wasu ayyukan bogi wadanda bai biya ba lokacin mulkinsa

The Punch ta ruwaito Garba Shehu, kakakin shugaban kasa na fadin haka a wata hira da yayi da wani gidan radiyon a Kano mai suna Express.

KU KARANTA: Yanzu haka: Yan Boko Haram sun kashe mutane 22 a kauyukan Borno#

Garba Shehu yace ayyuka da dama a rubuce kawai suke, yanzu ne gwamnatin Muhammadu Buhari ke aiwatar das, yayi misali da tagwayen hanyoyin da suka hada Kano da Katsina wadanda ya kira "ayyukan yaudara da karya wadanda yanzu ne zasu kasance." Yace:

"An bayar da kwangilaf tagwayen hanyoyin daga Kano zuwa katsina shekaru ukku da suka wuce daga gwamnatin data shude. Basu bada kobo ba domin fara aikin. Yanzu ne shugaba Buhari ya biya kashin farko na hanyar mai tsawon kilomita 75, kuma har an fara aikin."

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel