Yanzu-yanzu: A Kori Ministan Ilimi ko kuma…–ASUU

Yanzu-yanzu: A Kori Ministan Ilimi ko kuma…–ASUU

- Kungiyar Malaman jami’o'i watau ASUU ta bukaci Shugaban kas Muhammadu Buhari da lallai ya kori ministan Ilimi Malam Adamu Adamu

- Reshen kungiyar na Jami'ar gwamnatin tarayya na koyar da fasaha da ke Minna, ta ce ministan na shagulatin bangwaro da harkar ilimi, ba kuma shi da aniyar fardado da ilimin a Najeriya

Yanzu-yanzu: A Kori Ministan Ilimi ko kuma…–ASUU
Ministan Ilimi Adamu Adamu wanda kungiyar ASUU ke neman a sallame shi daga mukaminsa

Kungiyar malaman Jami’o’i ta bukaci shugaban Muhammadu Buhari da lallai ya kori Ministan Ilimi Adamu Adamu.

Kungiyar ta ce Ministan ya yi watsi da harkar ilimi da ke tabarbarewa, ba kuma shi da niyar yin wani abu na farfado da lalacewa da ilimin a kasar.

Wani reshen kungiyar ne na Jami’ar Fasaha ta gwamnatin tarayya FUTA da ke Minna, a jihar Niger ne ya yi wannan kira a wata sanarawa da  ya fitar, wacce kuma shugaban reshen Dakta Ndamisa Mohammed Attahiru ya sa hannu a kai.

Sanarwa ta ci gaba da cewa, da Ministan da gaske ya ke, da kungiyar ba ta shiga yajin aikin da ta ke yi a yanzu ba, ta kuma ce, Ministan ya ki ya saurari koke-koken kungiyar tare da watsi da wasikun da ta yi ta rubuta masa.

Game da matakin da kungiyar za ta dauka bayan yajin aikin na mako guda na gargadi da ta ke yi, sanarwar ta ce,  “muna da tattaunawar da mu ke yi da gwamnati na mako guda, da na bayan makwannin biyu, da kuma na bayan makwanni uku… idan har babu wani abin ku-zo-ku-gani bayan mako guda, zamu dora har zuwa bayan makwannin da muka diba, za mu tafi yajin aikin sai baba-ta-gani, kuma an sanar ministan domin babu wani abin boyewa”.

Sai dai wasu rahotannin na cewa, kwamitin ilimi na majalisar Wakiliai da kuma wasu mayan ‘yan kasar na iya baki kokarinsu na shiga tsakanin kawo karshen yajin aiki  da kuma yiwa tufka hanci.

Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel