Al’ummomin jihar Legas sunyi Tir da matakin Ambode

Al’ummomin jihar Legas sunyi Tir da matakin Ambode

Wasu al’ummomi a jihar Legas mazauna unguwar talakawa na Otondo Gbame da sauran unguwanni makwabtansu sunyi yi tofin Alatsine kan matakin rushe gidajensu da Gwamna Ambode ya dauka a satin daya gabata.

Al’ummomin jihar Legas sunyi Tir da matakin Ambode

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewar sai da yansanda suka fara sanya ma gidajen jama’an wuta a ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba kafin daga bisani aka zo da gingima gingiman motoci aka har guda tara aka rushe gidajen aka yi ma unguwar lebur.

Jama’an da yawansa ya kai 30,000 sun koma kwana akan kwalekwale cikin ruwa bayan an rushe musu gidajensu da wuraren sana’oi’insu.

Legit.ng ra dauko rahoton cewar “da safiyar ranar Lahadi 9 ga watan Nuwambar 2016 ne wasu gungun matasa da ake tsammanin gidan sarautar Elegushi ne suka turo su, suka fado unguwar Otodo Gbame dake gabar tafkin Legas, wanda mafiya mazaunin unguwar sun dogara ne da gamun kifaye. Shigowarsu unguwar keda wuya sai suka fara cinna ma gidajen unguwar wuta.

KU KARANTA: Shin Buhari zai kyale Dasuki yaje ta’aziyyar Mahaifinsa?

“yayin da al’ummar unguwar Otodo Gbame ke cikin jimamin ibtila’in daya samesu da yammacin ranar, sai ga takardan tashi zuwa ga ofishin yansanda na Ilasan don su sanar da mutanen yankin cewa za’a tashe su, sai aka manna takardan a wurare daban daban.”

Rahotanni sun bayyana cewar an cigaba da yin rusau a unguwar har cikin dare, zuwa safiyar ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba, a lokacin da manyan motocin suka karasa ruguza gidajen da wuta bai ci su ba.

Sai dai a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba ne al’ummar unguwar suka yi wata zanga zangar lumana zuwa ofishin Gwamna dake fadar gwamnatin jihar, inda suka bukaci a shawo kan matsalar, bayan acewarsu mutane 50 sun rasa rayukansu.

Taron jama’an sun fusata matuka, inda har ma suka dinga aika ma Gwamnan zagi kala kala, sakamakon halin da ya saka su.

Ga kadan daga cikin hotunan zanga zangar.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel