Boko Haram sun sake kashe wani kwamnadan Soja

Boko Haram sun sake kashe wani kwamnadan Soja

Hotunan wani kwamandan rundunar mayakan sojan kasa da kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram ta kashe a ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba sun bayyana.

Boko Haram sun sake kashe wani kwamnadan Soja
Laftanar kanar BU Umar

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar yan Boko Haram sun kashe Laftanar kanar B.U Umar ne a wani harin kwantan bauna da suka yi mai yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Adamawa zuwa jihar Borno.

Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewar motar da kanal Umar ke ciki ne ta daki wani kayan tashin bom da aka dasa akan hanya, daga nan sai ya sauko tare da sojojinsa don duba barnar da bom din yayi ma motar yakinsu.

KU KARANTA: Wata Daliba tayi bikin yajin aikin malaman Jami’a

Boko Haram sun sake kashe wani kwamnadan Soja

Daga nan ne sai maharani Boko Haram suka fito daga dajin gefen hanyar suka bude wuta akan kanar Umar da Sojojinsa, inda suka kashe Umar wanda shi ne kwamandan runduna ta 114 na bataliyan mayakan sojan kasa.

Wannan lamari ya faru ne akan hanyar kauyen Bitta zuwa Pridang na jihar Borno.

Boko Haram sun sake kashe wani kwamnadan Soja

A wani labarin kuma wani karamin Soja mai suna kofur Ibrahim Usman ya bukaci yan Najeriya dasu karrama sojoji kamar yadda suke yi ma yan matan Chibok, kofur Usman ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai yayin dayake jinyar raunukan daya samu sakamakon harin Boko Harama a ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel