Goodluck Jonathan yayi tsokaci kan mutuwar Dasuki

Goodluck Jonathan yayi tsokaci kan mutuwar Dasuki

- Goodluck Jonathan yayi jinjina ga marigayi Ibrahim Dasuki, ya kuma bayyana shi a matsayin mai kara kawo danko zumunci da zaman lafiya a kasa               

- Sanata Bruce yace mutuwar Dasuki kamar yaye haske ne a kasar nan                                                  

 - Za'ayi jana'izar Dasuki ranar talata 15 ga watan Nuwamba da misalin karfe 2 na rana kamar yadda addini ya tanada    

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana sakon ta'aziyyar shi ga iyalan Dasuki saboda rasuwar Alhaji Ibrahim Dasuki . Jonathan din wanda ya aika sakon gaisuwar ta sa ta shafin sa na Facebook.

Goodluck Jonathan yayi tsokaci kan mutuwar Dasuki

Yace " na tuna mai alfarma tsohon sarkin sarkin musulmi  a matsayin mutum mai son hada kan al'umma da kawo zaman lafiya, kuma uba wanda ke kokarin tabbatar da hadin kan Najeriya , yayi rayuwa mai tsawo, kuma zamu yi kewar rayuwar sa mai amfani.

Ina ta'aziyya ga iyalan sa, da rokon Allah ya bashi aljanna. Inji GEJ.

Kamar yadda sanata Bruce ya bayyana a sashen sadarwa na twitter yace, rasuwar tsohon sarkin musulmi Dasuki ta kasance kamar kamar an yaye  haske ne a kasar mu, muna fatar aljanna  ta zama makomar  shi.

Alhaji Ibrahim Dasuki wanda Ubane ga Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya rasu da shekara 93, ranar litinin 14 ga watan Nuwamba .

Dasuki tsohon sarkin musulmi a Sokoto kuma wanda ya hau wannan matsayin 18 a jerin  wadanda su rike sarautar.

Za'ayi janazar  Ibrahim Dasuki ranar talata 15 ga watan Nuwamba da karfe 2 kamar yadda addini ya tanada.

Za'ayi Sallah jana'izar a hubbaren shehu a garin Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel