Buhari yana cikin tsaka mai wuya dangane da

Buhari yana cikin tsaka mai wuya dangane da

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin tsaka mai wuya bayan mutuwar tsohon sarkin musulmi na Sokoto wato Ibrahim Dasuki.

Yan Najeriya sun bayyana a shafin yanar gizo cewar mutuwar Dasukin bai rasa nasaba da daukin da akayima yaron wato Sambo Dasuki, wanda suka daura alhakin hakan da cewar ramuwa ne Shugaba Buhari yayi sakamakon abunda sukayi masa shekaru 30 da suka wuce.

Buhari yana cikin tsaka mai wuya dangane da

Sambo Dasuki da Shugaba Buhari da Marigayi Ibrahim Dasuki.

Acewar bayanin da mutanen sukeyi, ya hada da cewar mutuwar na Dasukin ya biyo bayan daureshi da Buharin yayi na lokaci mai tsawo, kuma harma wani lokaci yasa akaje gidan Dasukin aka bincike gidan sa alokacin da baya kasar.

Gadai kadan daga cikin ra'ayoyin na jama'a a shafin na FaceBook.     Chukwuma Israel: Buhari ya kara kashe wani ran, waishin meye zai samu game da rayukan nan da yake kasewa?

Inda shi kuma Innocent Orobosa Enabele, yace Buhari bazai bari Dasuki ya halirci jana'izar babansa ba, saboda shima lokacin da mahaifiyar sa ta rasu alokacin mulkin soja na Babangida ba'a barshi yaje jana'izar ba.

Shi kuma Michael Okechukwu, cewa yayi, Bamuji dadin mutuwar mahaifin Sambo Dasuki ba, Amman kuma a sani yaron sa shima yayi sanadiyar mutuwan iyayen wasu da dama alokacin daya raba kudin makamai.

Shikuma Jonathan Chinasa Jay, cewa yayi, buhari yana kokarin jama kansa bakin jinine tare da iyalan sa dan haka yana da kyau yabar Sambo yaje jana'izar baban sa.

Saidai kuma rahoto ya bayyana cewar, hukumar farin kaya taba Sambo Dasuki damar yaje yaga gawar mahaifinsa. Inda ya bayyana cewar shi baya bukatar hakan, saidai a sakeshi gaba daya kamar yadda kotun Ecowas ta bada dama a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel