Farashin kayan masarufi sun jefa mutane cikin ukuba

Farashin kayan masarufi sun jefa mutane cikin ukuba

- Hukumar kididdiga ta kasa ta ce farashin kaya a Najeriya ya karu da kusan sama da kashi 18 bisa dari a cikin watan Nuwamba

- Ta ce farashin kayan ya yi tashin gwauron zabin da bai taba yi ba a cikin shekaru 11, wanda hakan wata alama ce ta karin matsin tattalin arziki a kasar

- Farashin da ya fi tashi shi ne na gidaje, da ruwan sha, da wutar lantarki, da na gas, da sauran makamashi, in ji hukumar

Farashin kayan masarufi sun jefa mutane cikin ukuba

Shi ma farashin kayan abinci ya tashi zuwa sama da kashi 17 cikin dari a watan Oktoba, idan aka kwatanta da kashi 16 da rabi a watan Satumba.

Najeriyar wacce memba ce a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, kuma mafi girman arziki a Afirka, na fuskantar matsin tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 25.

Ku Karanta: Shin Atiku zai iya Kada Buhari kuwa?

Faduwar farashin mai da yawan kai hare-hare kan bututan man a yankin Niger Delta na haifar da koma baya na danyen man da kasar ke hakowa.

Ya kuma haddasa karancin dalar Amurka, da hakan ya yi mummunan tasiri kan harkokin kasuwancin shigowa da kayayyakin ciyar da masana'antu a kasar.

A wani rahoton da aka fitar a farkon watan jiya ya na nuni da cewa Babban Bankin Duniya ya ce an samu raguwar matsananci talauci a daukacin duniya, duk kuwa da tafiyar hawainiyar da tattalin arziki ke yi wajen habaka.

Yawan mutanen da aka ayyana a matsayin matalauta na innanaha a shekarar 2013 sun kai miliyan dari takwas.

Hakan na nufin an sami ragin mutane miliyan dari daya, idan aka kwatanta da yawan matalautan a shekarar da ta gabaci 2013.

Bankin na duniya ya ce an samu cigaba a nahiyar Asia musamman ma kasar Sin da Indonesia da kuma India.

Sai dai Bankin ya yi gargadin cewa akwai bukatar kara zagewa wajen kawar da wagegiyar tazarar da ke tsakanin masu shi da matalauta.

Bankin ya kuma kara da cewa cimma burin bankin na kawo karshen talauci a fadin duniya a shekara 2030, ya ta'allaka ne ga kawar da rashin daidaiton da ke tsakanin mutane.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel