Dasuki ya ki ziyarar mahaifinsa tsohon sultan da yayi jinya saboda DSS

Dasuki ya ki ziyarar mahaifinsa tsohon sultan da yayi jinya saboda DSS

An rahoto cewa Sambo Dasuki, wani tsohon maiba shugaban kasa shawara a harkan tsaro a karkashin Goodluck Jonathan kuma dan tsohon Sultan na Sakkwato Ibrahim Dasuki, yak i ganin mahaifinsa da yayi jinya na wani lokaci yayinda yake tsare, Sahara Reporters ta rubuta.

A cewar wata majiya, hukumar yan sandan farar hula ta DSS ta ba Dasuki damar zuwa ganin mahaifinsa dake fama da tsananin rashin lafiya makonni biyu da suka wuce amma kanal din mai ritaya yaki amincewa da damar.

Dasuki ya ki ziyarar mahaifinsa tsohon sultan da yayi jinya saboda DSS
Ibrahim Dasuki da Sambo Dasuki

Dasuki ya dauki damar a matsayin yunkuri da hukumar DSS keyi na sakin sa zuwa dan wani lokaci sannan su kuma kama shi daga baya.

“An saki tsohon mai ba shugaban kasar shawara a harkan tsaro makonni biyu da suka wuce don ya ziyarci mahaifinsa dake fama da tsananin rashin lafiya, amma yaki amincewa da sakin da aka masa don ya ziyarci mahaifin nasa cewa ba zai amince da saki na dan lokaci kamar yadda kotun ECOWAS ta bada umarni ba” Sahara Reporters ta rubuta.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata maza ma su kasance a kitchen – Babangida Aliyu

Hatta Maman Daura dake kusa da fadar shugaban kasa, wanda ke auran kanwar Sambo ya kasa canja ma Dasuki ra’ayinsa a kan al’amarin yayinda ya tsaya a kan bakarsa.

Karshen jawabinsa a jama’a ya kasance a birnin Landan a watan Yuli na shekara 2015, bayan wani bincike da hukumar yan sandan farar hula suka gudanar a gidansa dake Sakkwato bayan sun kama dansa.

Sahara Reporters sun rubuta jawabin Ibrahim Dasuki, wanda ya mutu a ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba na karshe da yayi a jama’a, a lokacin da ya soki hukumar SSS da suka mamaye gidansa saboda kawai gwamnati na zargin dansa.

“Kwarai a kan dana ne, amma na bambamta da shi. Gidana ya bambamta da nashi gidan. Idan gwamnati na da wani abu a kan shi, taje ta binciki gidansa a Abuja amma ba wai gidana ba” marigayi Sultan na Sakkwato mai murabus ya bayyana wa BBC.

https://youtu.be/ZxG-FBqkJp4

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel