Ban saci kudi ba - Tsohon mataimakin shugaban kasa

Ban saci kudi ba - Tsohon mataimakin shugaban kasa

- Tsohon mataimakin shugaban Kasa, Atiku Abubakar yace shi ba barawo bane

- Atiku Abubakar yace idan ya saci kudi, Hukumar EFCC ta kama sa

- Sai dai ‘Yan Najeriya sun ce anya kuwa ace Atiku Abubakar bai saci kudi ba?

Ban saci kudi ba - Tsohon mataimakin shugaban kasa
Atiku Abubakar

 

 

 

 

 

 

 

Alhaji Atiku Abubakar, Turakin Adamawa ya rike Mataimakin Shugaban Kasar nan na shekaru takwas, lokacin Shugaba Obasanjo. Alhaji Atiku Abubakar din ba da Dan Siyasa ne, hamshakin dan kasuwa ne. Atiku yace shi bai saci kudi ba game da wani sabon zargi da ake yi masa.

A wata hira da Alhaji Atiku Abubakar yayi da Mujallar Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yace shi fa bai saci kudin kowa ba. Atiku Abubakar yace sharin da ake masa shine ya nada wasu Ministoci a lokacin Gwamnatin Obasanjo, Atiku Abubakar yace in dai wannan ne, ya wanke kan sa a Kotu.

KU KARANTA: Muna bayan Atiku Inji Gwamnatin Adamawa

Atiku Abubakar yace Kotu ta wanke sa sarai, don haka babu wanda ya taba samun sa da laifin sata a Kasar nan. Atiku Abubakar yace duk rikicin siyasa ne kurum ke kawo wannan maganganu. A littafin da Malam El Rufai ya rubuta, ya zargi Atiku Abubakar da laifuffuka na awon gaba da kudi, sai dai Atiku Abubakar din yace Nasir El Rufai ba kawo wata hujja ba.

Atiku Abubakar yace shi Malam Nasir El Rufai ne ma yayi kokarin kawo masa wasu hannun shi kuwa yace bai dace ba. ‘Yan Najeriya da dama dai suna ganin anya kuwa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel