Falana yace ya kamata gwamnati ta saki Sambo Dasuki

Falana yace ya kamata gwamnati ta saki Sambo Dasuki

- Wani Babban Lauya a kasar nan yace ya kamata gwamnatin tarayya ta saki Sambo Dasuki

- Femi Falana yace abin da ya dace shine gwamnati ta bi hukuncin Kotun ECOWAS da ta ce a saki Sambo Dasuki

- Kotun ECOWAS ta bada hukuncin cewa bai halatta gwamnati ta cigaba da tsare Sambo Dasuki ba

Falana yace ya kamata gwamnati ta saki Sambo Dasuki

Femi Falana

 

 

 

 

 

 

Wani Babban Lauyan Kasar nan, Femi Falana SAN yayi kira da Gwamnatin Tarayya da ta karrama umarnin da Kotun ECOWAS na wannan Yanki na Nahiyar Afrika ta bada na cewa a saki Tsohon mai bada shawara kan harkar tsaro na Kasar Sambo Dasuki.

Babban Lauya na Kasa Femi Falana yace don a saki Sambo Dasuki ba ya nuna cewa ana nufin ya je an gafarta masa ko ana nufin bai da laifi. Lauyan yace Kotun na ECOWAS ta yanke Hukunci cewa rike Sambo Dasuki ba tare da wani dalili ba, ya sabawa Tsarin mulki da dokar Kasa da kuma Tsarin Hakkin Bil’Adama na Nahiyar Afrika.

KU KARANTA: Farfesa Sagay ya fasa kwai

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Shugaba Buhari ya ba Hukumar da ke kula da binciken Sambo Dasuki umarnin karbo kudin da ya karkatar lokacin da ya ke rike da ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro lokacin Shugaban Kasa Jonathan Goodluck.

Kwanakin baya Kotun ECOWAS ta Nahiyar Afrika ta bada hukunci cewa bai halatta Gwamnati ta cigaba da tsare Sambo Dasuki ba ta kuma nemi Gwamnatin Tarayya ta biya Dasuki Naira Miliyan 15 na ci masa mutunci da lokaci.

 

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel