Jackie Chan ya ci kyautar Oscar

Jackie Chan ya ci kyautar Oscar

- Shahararren dan wasan kwaikwayo na Kasar China, Jackie Chan ya karbi lambar yabo

- An karrama Dan wasa Jackie Chan da sauran wasu ‘Yan wasan kwaikwayo a karshen wannan makon

- An ba Jackie Chan lambar girma ne a Garin Hollywood na Amurka

Jackie Chan ya ci kyautar Oscar

 

 

 

 

 

 

 

 

Shahararren dan wasan kwaikwayo, Jackie Chan

Ranar Asabar dinnan da ta wuce aka karrama Shahararren dan wasan kwaikwayo, Jackie Chan na Kasar Sin watau China. An ba shararren dan wasan lambar yabo ne saboda jaruntar sa a fagen wasa a Birnin Hollywood na Kasar Amurka.

Daga cikin wadanda aka ba lambar yabon akwai wani Editan Fina-finai, Anne V. Coates, da kuma wani Darekta, Lynn Stalmaster da wani kwararren mai hada fim na Amurka, Fredrick Wiseman. Sai shi dan wasa Jackie Chan kan sa. Jaridar XINHUA net ta Kasar China ta dauko wannan labara.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya taya 'yan wasa murna

An ba wadannan gwanaye lambar girma ne saboda irin rawar ta suka taka a fagen wasan kwaikwayo. Wannan ne karo na takwas da aka yi irin wannan taro na lambar girma na Gwamnoni da ake yi a Hollywood. Masu hada abin suka ce ba za a manta da irin su Jackie Chan ba.

Jackie Chan kwararren dan wasa ne, marubuci, mai hada fim, kuma Darekta. Tun yana dan shekara 8 yake wasan kwaikwayo a Hong-Kong, kafin ya fita duniya gaba daya. Jackie Chan yace ba zai taba manta wannan rana ba, bayan ya karbi kyautar sa. Yace abin kamar a mafarki. Jackie Chan ya fi shekara 56 yana wasan fim.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel