Sojojin na ci gaba da yakar tsageru a Bayelsa

Sojojin na ci gaba da yakar tsageru a Bayelsa

- Sojojin Najeriya na ci gaba da yakar tsagerun yankin Niger da ke Bayelsa a inda suka samu nasarar hallaka daya daga cikin shugabanninsu a yankin

- Tsagerun na sajewa da sajewa da mazauna yankin da zaran sojojin sun cim masu, mazauna na tsoron nuna su ga jami’an tsaro don tsoron su

Sojojin na ci gaba da yakar tsageru a Bayelsa
Rundunar Sojin Najeria a yankin Niger Delta na farautar tsageru a yankin

Rundunar sojin Nejeria na samu galaba kan tsagerun Niger Delta a kokarin da ta ke na kawo karshen fashe-fashen butun Mai a yankin.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa, rundunar hadin gwiwa ta JTF ta kuma kashe wani jagoran wanda tsagerun da ka fi sani da Edoboy biyo bayan fadada ayyukansu zuwa cikin ruwa, harin ya biyo bayan hare-haren da tsagerun ke kaiwa kan bututun Mai duk da tattaunawar sulhu da su suke yi da gwamantin tarayya.

Jaridar ta kuma rawaito cewa,  an umarci sojojin da su gano su kuma lalata duk wani sansani da 'yan ta'addan ke amfani da shi a yankin, a nan ne kuma suka hadu da wani gungun tsagerun  a wani sansani mai suna Sand-Sand Fishing Camp, suna kokarin dawo da wani sansani da a ka lalata.

KU KARANTA KUMA: Kamfanin shell ya rufe ma'aikatantar sa a yankin Neja Delta

Wani da muka samu labari a wajensa mai suna Buhari ya ce, bayan gama tattara bayanan sirri, sojojin sun afkawa sansanin har ta kai su da harbe-harbe, ya ce, “lamarin bai zo da sauki ba saboda tsagerun sun tara makamai sosai. Amma duk da haka mun murkushe su, kuma mun kashe daya daga cikin shugabanninsu wanda a ka fi sani da Edoboy. Kuma har yanzu muna bibiyar wadanda suka gudu cikin ruwa."

Majiyar ta ci gaba da cewa, “duk lokacin da mu ka bi su cikin mutane su ke shiga su saje hakan ke sa gano su na mana wahala. Mutane kuma na tsoron nuna su. Su kuma'yan ta'addan na yin amfani da mutanen su zargi JTF da take hakkin bil adama. Mu kwararru ne ba kuma za mu aikata duk wani abu da zai bata sunan sojoji ba.”

Ita kuwa kungiyar tsagerun ta Niger Delta Avengers yi alwashin kaddamar da yaki cikin kwanaki bakwai idan gwamantin Buhari ba ta biya mata bukatun ta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel