Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

- Yan wasan kwallon kafa na kasar Algeria sun sauka garin Uyo babban birnin Akwa-ibom, domin faffata wasan da zai gudana a ranar Asabar dinnan mai zuwa da kungiyar Super Eagles ta Najeriya, domin samun nasarar zuwa gasar cikin kofin duniya.

- Yan Afirican na yamman dai sun samu jagorancin shugaban hukumar kwallo ne na kasar su wato Mohamed Raouraouia.

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Wasu yan kasan Algeriya kenan suna dauke da jakunkunan su da kuma matasan kai.

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Yan wasan kasar Algeriya kenan suna dauke da jakunkunan su da matasan kai.

Amman abun mamakin shine, yan kasar Algerian sun iso Najeriya ne tare da ruwan shan su da abincin su dakuma kayayyakin baccin su.

Sun dai zone da jirgin Chartered a ranar Alhamis da yamma wato 10 ga watan Nuwamba da misalin karfe 6:45 na yamman, kuma manyan hukumomin kwallon kafa na Najeriya suka tarbe su Wato (NFF).

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Yan wasan kasar Algeriya suna dauke da jakunkunan su da kuma fulallukan su.

Yan dai Afirikan na Arewa nan da nan aka kaisu otel din nan na Le Meridian, inda yan wasan kwallon Najeriya suke, kuma zasuyi atisaye gobe a filin wasa na Godwill Akpabio dake garin Uyo.

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Mahrez da sauran yan wasan kasar Algeria dauke da matashin kwanciyar su.

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Yan wasan kwallon Algeria dauke da matashin kwanciyar su.

Sai dai kuma sabon kocin nasu mai suna George's Leekens, yana fama da matsalar rashin lafiya na wasu manyan yan wasan sa, kamar Ryad Boudebouz, da kuma dan wasan baya na Napoli wato Faouzi Ghoulam, yana cikin halin kila wa kala nayin wasa, saboda yana fama da ciwo a gwiwar sa.

Sai dai kuma wasan da za'a buga a ranar Asabar dinnan mai zuwa, zai gudana ne da misalin karfe 5 na yamman.

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Dan wasan kasar Algeria ya sauka garin Uyo da matashin kwanciyar sa.

Indai za'a iya tunawa yan Algeria sun buga 1-1 ne da kasar Camaroon a garin Bilda, a inda kuma Nageriya ta lallasa kasar Zambiya daci 2-1 a garin Ndola.

Algeria sun sauka a garin Uyo da abincinsu da ruwan su

Haka kuma sun sauka da ruwan shan su da kuma abincin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel