Shanaye sun kwace filin jirgin sama a Owerri

Shanaye sun kwace filin jirgin sama a Owerri

- Wani direban jirgin sama ya fasa sauka saboda shanayen da ya gani a titin jirgi a Owerri, wani babban birnin jihar Imo a yankin Kudu maso gabashin kasar

- Sai da jami’an tsaro suka kora shanayen kafin direban ya samu sauka

- Fasinjoji sun yabawa matukin jirgin da kwarewarsa wajen kare hadari

Shanaye sun kwace filin jirgin sama a Owerri

An samu wata tashin hankali tsakanin fasinjojin jirgin AirPeace yayinda shanaye suka hana jirgin sama sauka a titin jirgin filin jirgin saman Sam Mbakwe da ke Owerri,jihar Imo.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa daya daga cikin fasinjojin mai suna Mr. Richard Akinnola yace sai da direban jirgin ya fara sauka sannan ya lura cewa shanaye sun cika cikin filin jirgin.

KU KARANTA: Basketmouth zai fito takaran zaben shugabancin kasar Najeriya a 2019

Fasinjoji sun shiga halin fargaba yayinda direban ya fasa sauka har sai lokacin da jami’an tsaro suka kora shanayen sannan ya samu sauka da su.

Irin wannan abu ya faru kwanakin baya a babban filin jirgin saman fatakwal inda wata jirgin Air France tayi kicibis da shanaye wanda ya sabbaba lalacewan wasu sassan jikin jirgin, amma gwamnatin tarayya ta biya kudin gyara.

Jama’a sun yabawa direban jirgin da kwarewarsa wajen kawar da mumunan hadarin da fasinjoji ke tsoron faruwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel