Sojoji sun hallaka mata yan kunar bakin wake

Sojoji sun hallaka mata yan kunar bakin wake

Jami’an rundunar mayakan sojan kasa dake garin Maiduguri sun harbe wasu yan mata yan kunan bakin wake su Uku dake dauke da bamabamai a jikkunansu a ranar Juma’a 11 ga watan Nuwamba.

Sojoji sun hallaka mata yan kunar bakin wake

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar kusan duk garin Maiduguri sai da aka ji karar tashin bamabaman yayin daya tashi da yan kunan bakin waken bayan Sojoji sun harbe su.

Kaakakin Hukumar yansandar jihar Victor Ishaku ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace “da safiyar yau Juma’a da misalin karfe 5:30 na asuba, jami’an soja dake gudanar da sintiri a kauyen Umariri dake kusa da Mulai hanyar shiga Maiduguri suka hangi wasu mata su Uku yan kunan bakin wake.

KU KARANTA:Buhari ya nada dan-uwan Sarkin Ife a mukamin Jakada

“jami’an Sojan basu yi wata wata ba suka bindige su, wanda hakan yayi sanadiyyar fashewar bom din dake jikin mata biyu a cikinsu, amma ya kashe su duka ukun. Jami’an yansanda sun warware bom na ukun da bai tashi ba”

Sojoji sun hallaka mata yan kunar bakin wake

Kwamishinan yansanda ya danganta yawan hare hare da ake samu a yanzu ga shigowa lokacin bazaar, yace wannan ke baiwa yan ta’addan daman shigowa gari ta cikin dazuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel