Rikicin APC: Tinubu zai kafa sabuwar jam’iyya

Rikicin APC: Tinubu zai kafa sabuwar jam’iyya

- Wasu mambobin jam’iyyar APC a yankin kudu maso yamma suna kokarin barin jam’iyyar APC

- Sanata Adesoji Akanbi,yace yan Najeeriya zasu fara ganin wasu gamayye-gamayye na jam’iyyu

- Mataimakin shugaban jam’iyyar ta kasa (yankin kudu), Hilliard Eta,yace jam’iyyar na sane da wasu kulle-kulle da wasu keyi domin raba kan jama’a

Rikicin APC: Tinubu zai kafa sabuwar jam’iyya
APC Logo

Wani mamban jam’iyyar APC kuma mabiyi Bola Tinubu ya bayyana cewa suna shirin kafa wata sabuwar jam’iyyar da zata kwace mulki a shekarar 2019.

An sa ran wata gagarumar shekewa daga jam’iyyar APC musamman a yankin kudu maso yamma yayinda mabiya Bola Tinubu na ganawa domin tattaunawa akan yadda zasu kafa wata sabuwar jam’iyyar kafin 2019.

KU KARANTA: Zubar hawaye: An binne yara 6 bayan kishiyar uwarsu ta basu guba a Anambra (hotuna)

Daga cikin masu ganawar akwai gwamnoni, yan majalisu musamman sanatoci daga yankin, wadanda suna zange dantse domin tabbatar da cewa ba za’a yaudaresu ba a gwamnatin gobe.

Sanata Adesoji Akanbi ya tabbatar da hakan ga jaridar Punch a ranan alhamis, 10 ga wtan Nuwamba ,cewa yanNajeriya zasu ga sabbin jam’iyyu da maja.

Akanbi yace wasu kososhi wadanda suka taimaka wajen kafa jam’iyyar bas u jin dadin yadda wasu abubuwa ke faruwa yanzu da jam’iyyar ta dau ragamar mulki kuma suna neman mafita.

Tabbatar da haka, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (yankinkudu), Hilliard Eta, ya fada ma jaridar Punch cewa suna sane kulle-kullen da wasu mambobin jam’iyyar keyi domin raba kan mambobin jam’iyyar.

“Muna sane da wasu motsisika da wadansu masu son shekewa keyi. Sun fara hakan ne ta hanyar raba kan jam’iyyar domin samun mafitar shekewa amma su sani cewa muna nan daram dam. Wadanda ke son shekewa ga fili ga mai doki, na fi son su wuce ma domin mu samu damar karfafa jam’iyyar mu.

“Idan suna son kafa sabuwar jam’iyya ne, Allah basu sa’a; zamu hadu a 2019.

Ku biyo mu a shafin Twitter, shine: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel