Kasar Singapore za ta aika wani Dan Najeriya lahira

Kasar Singapore za ta aika wani Dan Najeriya lahira

An kama wani Dan Najeriya da laifin safarar kwayoyi a kasar Singapore

Yanzu haka, za a aika wannan mutumi lahira

Kungiyar Amnesty na neman a rage wannan hukunci mai zafi

Kasar Singapore za ta aika wani Dan Najeriya lahira

 

 

 

 

 

Kasar Singapore ta samu wani Dan Najeriya mai suna Chijoke Obioha da laifin safarar kwayoyi a cikin Kasar. An samu Mista Chijoke da aikata wannan laifi ne tun shekarun baya can da suka wuce. Yanzu haka an yankewa wannan ta’aliki hukuncin kisa har lahira.

Kungiyar Amnesty na kokarin ganin sauran Kasashen duniya sun sa baki a rage wannan hukunci da kisan rai. A irin wadannan Kasashe dai duk wanda aka kama da laifin harkar kwayoyi, yak an bakunci lahira ba tare da wata-wata ba. An dai kama Chijoke Obioha ne dauke da kwayoyi a Ranar 9 ga Watan Afrilun 2007, tun wannan lokaci ake ta gwabza shari’a.

KU KARANTA: Musulamai sun shiga bala'i a duniya

Mista Chijoke Obioha yayi digiri a fannin Kimiyyar sinadarai a Jami’ar Benin ta Najeriya. An kama sa da muggan kwayoyi a jikin sa da kuma mabudan wasu wuraren da aka boye wasu kwayoyin da aka haramta.

Kungiyar Amnesty ta duniya dai tana neman ayi afuwa ga wannan mutumi, Amnesty tana ganin cewa kama mutum da kwaya bai kai laifin da za ayi kisan rai ba. An dai bayyanawa iyalin sa cewa, dan su zai bakunci lahira babu wata makawa. A kasar Singapore idan aka kama mutum da kwayoyi na sama da rabin kilogram, to lahira za tayi bako.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel